
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Kano Alliance for Democracy and Development ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa hoɓɓasarsa wajen ciyar da dimukraɗiyya da shugabanci na gari gaba a Jihar Kano.
Ƙungiyar, wadda manufarta ita ce ƙarfafa haɗin kai don samar da ci-gaba a Kano kuma cibiyar kasuwanci, siyasa da ɗaukar nauyi, ta ce Kano sama take da kowane mutum kuma al’amuran kwanan nan sun tabbatar da haka.
Don haka ne ta jinjina wa gwamnan jihar bisa tabbatar da cewa shi ɗan dimukraɗiyya ne na gaskiya wanda hakan ya sa ya zaɓi maitaimakinsa ta bin hanyoyin da ke nuna tsare gaskiya da adalci.
A cewar ƙungiyar, zaɓar Murtala Garo ya nuna cewa dimukraɗiyya ta yi nasara domin shi ne abin da al’umma suke buƙata musamman ‘yan APC, wanda gwamnan ya yi amfani da hikima wajan tabbatar da hakan.
Haka kuma, ta roƙi masu neman muƙamin da su haƙura da buƙatunsu tare da haɗa kai da gwamnan da sabon mataimakin nasa wajen yin aiki tare domin ciyar da jihar da al’ummarta gaba.
