Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana wasu daga cikin nasarorin da dakarun sojin Nijeriya suka samu a yaƙi da ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar nan, tare da sukar masu mayar da hankali kan gazawa kawai ba tare da la’akari da irin nasarorin da ake samu ba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce manufarsa ita ce wayar da kan jama’a kan irin ƙoƙarin da dakarun sojin ke yi a fagen yaƙi da ta’addanci.
Onanuga ya ce wasu daga cikin ’yan Nijeriya kan fi mayar da hankali kan hare-hare, garkuwa da mutane da fashe-fashe, suna watsi da nasarorin da ake samu, yana mai cewa hakan na rage ƙwarin gwiwar dakarun da ke sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa.
Ya jero wasu daga cikin nasarorin da aka samu, ciki har da ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su a Jihar Benuwai bayan wani samame da aka kai a dajin ƙaramar hukumar Ohimini. Ya bayyana cewa mutanen da aka ceto sun samu kulawar likitoci sakamakon raunukan da suka samu yayin da suke hannun masu garkuwa da su.
Haka kuma, ya ce dakarun sun samu nasarori a jihohin Filato da Benuwai inda suka kama wasu da ake zargi da aikata laifuka, ciki har da masu safarar makamai da kuma masu hannu a rikice-rikicen ƙabilanci.
A wani farmaki da aka kai a Jihar Filato, dakarun sun samu nasarar raunata wasu ’yan bindiga uku bayan sun kai hari kan sojoji a yankin Bassa. Haka kuma, an kama wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a kashe-kashe tare da ƙwato makamai da alburusai.
Rahotannin sun kuma nuna cewa dakarun sun gudanar da samame a wasu ƙauyuka, inda suka gano gawar wani makiyayi tare da ceto shanu da dama da aka sace. A wasu lokuta kuma, sun yi nasarar daƙile yunƙurin sace dabbobi tare da ƙwato su daga hannun ’yan ta’adda.
A yankin Arewa maso Gabas, dakarun sun ci gaba da samun nasarori a yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da ISWAP, inda suka daƙile hare-hare tare da kama masu kai wa ’yan ta’adda kayan aiki.
Haka kuma, a wasu jihohi kamar Edo, Sokoto da Kogi, an samu nasarori wajen daƙile garkuwa da mutane da kuma kama waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, lamarin da ya nuna irin muhimmancin tattara bayanan sirri da haɗin kai da al’umma.
A yankin Kudu maso Gabas kuwa, dakarun haɗin gwiwa sun lalata wasu abubuwa masu fashewa tare da hana su haddasa illa ga jama’a.
Onanuga ya jaddada cewa duk da cewa yaƙi da ta’addanci ba zai ƙare nan da nan ba, rundunar sojin Nijeriya na samun gagarumin ci gaba ta hanyar amfani da dabarun zamani da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da kuma ƙasashen duniya.
Ya yi kira ga al’umma da su riƙa yaba wa dakarun soji kan ƙoƙarinsu maimakon mayar da hankali kan suka kawai, yana mai cewa fahimtar ƙalubale da nasarori baki ɗaya na da muhimmanci wajen ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a ƙasar nan.
