Majalisar Dokokin Kano ta gayyaci Shugaban SUBEB kan zargin rashin gamsuwa da ɗaukar ma’aikata

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci Shugaban Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB), Alhaji Yusuf Kabir, domin ya bayyana a gabanta kan zargin rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da aikin daukar sabbin ma’aikata na baya-bayan nan.

Matakin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan majalisar suka nuna damuwa kan yadda aka gudanar da aikin, inda suka bukaci a sake duba tsarin domin tabbatar da an yi komai bisa gaskiya, adalci da kuma bin ƙa’ida.

Da yake gabatar da ƙudirin nuna rashin gamsuwa a zauren majalisar, ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Dambatta, Hon. Murtala Musa Kore, ya bukaci majalisar da ta shiga lamarin tare da tabbatar da an sake nazarin yadda aka gudanar da daukar ma’aikatan.

Hon. Kore ya bayyana cewa akwai ƙorafe-ƙorafe daga wasu masu neman aiki, waɗanda ke zargin cewa ba a bi tsarin gaskiya da adalci ba wajen tantance sunayen waɗanda aka dauka, lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin al’umma.

Bayan gabatar da ƙudirin, majalisar ta amince da gayyatar shugaban SUBEB domin ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka gudanar da aikin, tare da bayyana tsarin da aka bi wajen daukar ma’aikatan.

Majalisar ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da bin diddigin lamarin domin tabbatar da cewa dukkan matakan gwamnati ana gudanar da su bisa gaskiya, adalci da kuma bin doka.

Ana sa ran cewa bayan bayyanar shugaban SUBEB a gaban majalisar, za a dauki matakan da suka dace, ko dai domin gyara kura-kuran da aka samu ko kuma tabbatar da sahihancin aikin daukar ma’aikatan

By ukarofi