Trump ya tsallake rijiya da baya yayin farmakin bindiga a Fadar White House

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An gaggauta fitar da Shugaba Donald Trump na Amurka da Matarsa, Melania Trump daga wajen taron cin abincin dare na shekara-shekara na wakilan Fadar White House da aka saba yi a Birnin Washington D.C a ranar Asabar a lokacin da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta ana tsaka da shagali.

Al’amarin ya faru ne a daidai wajen da jami’an tsaro ke tantance mahalarta, inda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa tare da buɗe wa jama’ar wajen wuta.

Haka kuma, wani jami’in sirri ya tsallake rijiya da baya bayan harbinsa da aka yi a lokacin da yake sanye da rigar kariya.

Tuni dai jami’an tsaron da ke wajen suka hanzarta fitar da Shugaba Trump da matarsa da wasu manyan jami’an gwamnati daga wajen yayin mutane sama da 2,600 da suka halarci wajen suka shiga cikin firgici.

An ga yadda baƙin suke fakewa a ƙarƙashin teburan da aka jera yayin da jami’an tsaron suka yi ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali da lumanar al’umma.

Daga cikin waɗanda jami’an suka tilasta wa ɓuyar akwai manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da: Sakataren gwamnati, Marco Rubio; Sakataren Lafiya, Robert F. Kennedy Jr.; da kuma Sakataren Harkokin Cikin Gida, Doug Burgum.

By Babaji