Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar gudanarwar Katsina United ta gargaɗi ‘yan wasa da jami’an da ke cikin tsarin karɓar albashin a ƙungiyar,kan hana su shiga ko wakiltar wata ƙungiya ba tare da izinin ta ba a rubuce.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Surajo Baba Malumfashi, ya faɗi haka a wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Malam Nasiru Gide.
Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United yayi gargaɗin duk ɗan wasan da aka samu da wannan laifi ya kuka da kansa.
Sirajo Malumfashi yayi kira ga ɗaukacin ‘yan wasan da jami’an ta da su cigaba da mutunta dokoki da ƙa’idojin ƙungiyar.
