Faɗaɗa matatata zai samar da aiki ga ƙwararru 95,000 – Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa shirin faɗaɗa matatar man Dangote zuwa ƙarfin sarrafa ganga miliyan 1.4 a kowace rana zai samar da aikin yi ga ma’aikata masu ƙwarewa sama da 95,000 a lokacin da aikin ginin ya kai ƙololuwa.

Dangote ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako a Legas, yayin da aka karrama shi da lambar girmamawa ta ‘Honorary Fellow daga Nigerian Academy of Engineering’, inda ya bayyana wannan aiki a matsayin wani muhimmin mataki na sauya fasalin masana’antu a Nijeriya.

Ya ce, faɗaɗa matatar na nuna ƙudirin kamfaninsa na inganta harkokin injiniyanci, samar da ayyukan yi, da kuma bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa.

A cewarsa, “Wannan karramawa na da matuaar muhimmanci domin tana nuna irin ƙoƙarin da muke yi a masana’antu, musamman wajen ɗaukar injiniyoyi da ƙwararru. A lokacin da aikin faɗaɗa zai kai ƙololuwa, muna sa ran samun ma’aikata kusan 95,000 a wurin aiki, kuma hakan zai ci gaba da ƙaruwa.”

Bayan kammala aikin, ana sa ran matatar Dangote za ta zarce matatar Jamnagar da ke ƙasar Indiya, ta zama mafi girma a duniya, abin da zai ƙarfafa ƙarfin tace man fetur na Nijeriya.

Dangote ya ƙara da cewa, aikin zai dogara ne sosai kan ƙwarewar ‘yan Nijeriya, inda zai buɗe ƙofofi ga injiniyoyi, masu fasaha, masu sana’o’i da sauran ƙwararru.

Baya ga samar da aikin yi, ana sa ran wannan faɗaɗa zai ƙara bunƙasa masana’antu na cikin gida, inganta musayar fasaha, da ƙarfafa sashen mai da iskar gas na ƙasar. Haka kuma zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje, tare da ƙara tanadin kuɗaɗen waje ga tattalin arzikin Nijeriya.

A nasa ɓangaren, shugaban Makarantar Injiniypyi ta Nijeriya, Injiniya Farfesa Rahamon Bello, ya bayyana karramawar da aka yi wa Dangote a matsayin abin da ya dace, yana mai cewa tasirin da ya kawo ya wuce gina ababen more rayuwa kaɗai.

By ukarofi