Rikicin APC a Gombe ya yi ƙamari yayin da Gwamna Inuwa da Sanata Goje ke kafsawa kan tikitin sanata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu sabon rikicin siyasa acikin jam’iyyar APC a Jihar Gombe yayin da Gwamna Inuwa Yahaya da magoya bayan tsohon gwamnan jihar kuma sanata a yanzu, Ɗanjuma Goje suka bayyana muradin yankar tikitin sanatar Gombe ta Tsakiya a zaɓen 2027.

Wannan al’amari ya samo asali ne a lokacin da aka ayyana Mohammed Ahmadu Deba a matsayin ɗan takarar kujerar sanata a mazaɓar a matakin yarjejeniyar ‘ya’yan jam’iyya, lamarin da zai ba shi damar maye gurbin Sanata Goje, wanda ya haifar da ɓaraka a tsakanin masu biyayya ga Gojen.

Masu biyayyan na ganin wannan mataki a matsayin abin da ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022 musamman ganin hanyoyin da aka bi wajen ɗaukarsa.

Magoya bayan tsohon gwamnan sun yi watsi da matakin a fili, inda suka bayyana hanyar da aka bi a matsayin mataki mai alamar tambaya a shari’ance.

A cewar wata takarda daga Sa’idu Mu’azu Kumo, wato ɗan ɓangaren Goje, zaman yarjejeniyar tsayar da ɗan takarar da aka yi a Gidan Gwamnatin Gombe bai samu halartar wasu ‘yan takara da aka tabbatar da su ba.

Sun bayyana cewa, ware wasu ‘yan takara wajen ɗaukar matakin duk da cewa sun sayi fom ya nuna sakamakon ya haramta, suna gargaɗin ƙaƙaba wani ɗan takara ka iya haifar da taka dokar zaɓe da kuma barazanar ga dimukraɗiyya a matakin cikin jam’iyyar.

By Babaji