Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
A wani gagarumin sauyi da ya girgiza fagen siyasar Jihar Gombe, Jam’iyyar APC ta bayyana tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya, Mohammed Ahmed, a matsayin dan takararta na Sanatan Gombe ta tsakiya gabanin zaɓen 2027, tare da janye tsohon gwamna kuma sanata mai ci, Sanata Danjuma Goje, daga takarar.
Wannan mataki ya biyo bayan jerin shawarwari da tuntuɓa da aka gudanar tsakanin manyan shugabannin jam’iyyar, sarakunan gargajiya da wakilan al’umma daga ƙananan hukumomin Yamaltu/Deba da Akko, wadanda ke cikin mazabar Gombe ta tsakiya.
Mohammed Ahmed, wanda aka fi sani da “Jarman Deba,” ya samu wannan matsayi ne sakamakon yadda aka bayyana shi a matsayin mutum mai ƙwarewa, ladabi da kuma cikakken fahimtar al’amuran tsaro da shugabanci, la’akari da tarihin aikinsa a rundunar ‘yan sanda.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar “A Call to Action” ta fitar ta bakin shugabanta, Ambasada Benjamin Abner Mamman, ta bayyana wannan mataki a matsayin “babbar nasara da za ta ƙara karfin APC a yankin Gombe ta tsakiya.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, hadin kai, fahimtar juna da shawarwari masu zurfi ne suka kai ga cimma wannan matsaya, inda ta jaddada cewa an zaɓi Ahmed ne bisa la’akari da cancanta da kuma buƙatar ci gaban yankin.
Haka kuma, kungiyar ta yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya da sulhu a cikin jam’iyyar, tana mai cewa hakan ya taimaka matuƙa wajen cimma matsaya ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa sarakunan gargajiya, dattawa, mata da matasa sun taka rawar gani wajen tabbatar da wannan matsaya ta bai ɗaya, wadda ake ganin za ta kawo sabon salo a siyasar yankin.
A cewar Mamman, “zaɓen Mohammed Ahmed yana nuna ƙudurinmu na tafiya tare da haɗin kai domin gina makoma mai inganci ga al’ummar Gombe ta tsakiya.”
Ya kuma buƙaci al’ummar Yamaltu/Deba da Akko da su ci gaba da mara wa APC baya domin tabbatar da nasara a zaɓen 2027.
Masu nazarin siyasa na ganin cewa wannan mataki na iya sauya yanayin takarar Sanata a yankin Gombe ta tsakiya, yayin da ake hasashen sabuwar fafatawa mai ƙarfi a zaɓen mai zuwa.
