Daga JOHN D WADA a Lafia
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Hon. Silas Ali Agara ya bayyana a hukumance niyyar sa ta tsayawa takarar kujerar sanata ta Arewacin jihar Nasarawa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Silas Agara wanda kwanan nan ya sauka daga muƙamin Daraktan Janar na hukumar samar da aikin yi na tarayya wato NDE domin amsa abin da ya kira “kiran gaggawa” daga mutanen mazaɓarsa.
Da yake jawabi ga kwamitin gudanarwa na jihar na APC a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia a ranar Alhamis Hon. Agara ya roƙi shugabannin jam’iyyar da su tabbatar da cewa dimokuraɗiyyar cikin gida ta yi aiki.
Ya kuma buƙaci shugaban jam’iyyar na Jihar Dr. Aliyu Bello da ya tabbatar da cewa tsarin zabar ‘ɗan takara ya kasance a bayyane kuma ba tare da nuna son kai ba.
Yace “Na fara tafiya da zan kira tafiyar mishan ta Kirista domin ba da gudummawa ta wajen ci gaban wannan Jihar.
“Domin amsa kiran mutanenmu na yanke shawarar ajiye muƙamina. Ina yin haka ne domin girmama kiran mutanenmu da kuma ƙara wa siyasar jihar daraja.
“Ga ni Silas Agara ban fafata da kowa kan wani dandali ba. Dandalin ya yi girma sosai domin kowa ya nuna kuma ya tabbatar da darajar sa,” in ji shi.
“Ayyukanmu a nan a bayyane ne: domin sanar da ku a hukumance game da burin mu, da kuma samar da filin wasa mai daidaito ga kowa,” in ji Agara ga kwamitin.
“Na yi imani a matsayin mu ‘yan jam’iyya, ya kamata mu yi wasa bisa ƙa’ida. Za mu kasance a shirye mu bi ƙa’idojin jam’iyyar,” in ji shi.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa hanyar zuwa 2027 za ta kasance mai wahala yana mai lura da cewa jam’iyyar “ba ta tsira” daga matsaloli.
A cewarsa haɗin kai ne kawai zai tabbatar da cewa APC ta riƙe kujerar mulki.
Da yake mayar da martani shugaban APC na jihar ta Nasarawa Dr. Aliyu Bello ya yabawa jarumtakar Agara yana mai lura da cewa ba abu ne mai sauƙi ba ga ‘ɗan siyasa ya sauka daga muƙamin tarayya mai tsaro domin shiga fafutukar siyasar gida.
“Mutum ne mai jarumta mai hangen nesa kuma mai son mutanensa zai sauka daga muƙamin tarayya mai wa’adin shekaru ya dawo gida ya yi hidima,” in ji Bello.
Da yake amsa kiran a yi adalci Bello ya ba Agara da magoya bayansa tabbacin tabbatacce kuma tsari na gaskiya a yayin duka zaɓukan fitar da gwanayen ‘yan takarar jam’yyar All Progressive Congress APC din a zaɓuka masu zuwa na 2027.
“Tabbatar da filin wasa mai daidaito wannan ina so in tabbatar muku da kowane ɗan takara shi ne babban aikin mu APC a jihar nan ƙarƙashin jagoranci na za ta tabbatar da an bi ƙa’idojin jam’iyyar har zuwa ƙarshe. Za mu Kuma tabbatar da an ba kowane ɗan takara dama ta adalci,” in ji shi.
