Sojoji sun ceto yara da aka sace, sun cafke ‘yan ta’adda da masu kai musu bayanai a Arewa maso Gabas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation HAɗIN KAI a Arewa maso Gabas sun kama wasu da ake zargi da aikata ta’addanci, wani mai kai wa Boko Haram/ISWAP bayanai, da kuma dillalan ƙwayoyi a wasu hare-haren da suka kai a yankin.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar.

A cewar sanarwar, dakarun da ke aiki a Ngamdu, Jihar Yobe, sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da ta’addanci, wato Haruna Adamu mai shekaru 32 da Ibrahim Adamu mai shekaru 20.

Kayayyakin da aka samu a hannunsu sun haɗa da wayoyin hannu, na’urar ajiyar wuta (power bank), katin shaida, wasu sinadarai da ake zargi haramtattu ne, layu da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa waɗannan mutanen sun tsere ne daga Jihar Zamfara zuwa Jihar Yobe.

A wani samame na daban, dakarun Bataliya ta 254 sun kama wani da ake zargi mai kai wa Boko Haram/ISWAP bayanai, mai suna Ali Muhammad, a kasuwar Ngamdu.

An ce mutumin yana cikin jerin waɗanda ake sa ido a kansu, kuma an same shi da kuɗi, wayar hannu, katunan shaida, layu, wuƙa, da wani littafi da ke ɗauke da lambobin waya na waɗanda ake zargi da alaƙa da ‘yan ta’adda.

Rundunar sojin ta bayyana cewa wannan kamun babban ci gaba ne wajen dakile hanyoyin tattara bayanan sirri na ‘yan ta’adda.

Haka kuma, dakarun sun kama wasu dillalan kwayoyi guda biyar a wani samame na dare da suka kai a yankin Mubi na Jihar Adamawa. An same su da alburusai, kuma a halin yanzu ana ci gaba da bincike a kansu.

A wani ɓangare na daban, dakarun tare da haɗin gwiwar ‘yan Civilian Joint Task Force sun ceto wasu yara biyu da aka sace, Barnabas Apagu mai shekaru 12 da Ruth Apagu mai shekaru 10, a ƙaramar hukumar Madagali.

An ce ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.

Haka kuma, dakarun sun gano wata gurneti a yankin Kukareta na Jihar Yobe, wacce ake zargin ‘yan ta’adda ne suka bari yayin da suke tserewa.

Babban kwamandan rundunar sojin ya yaba wa dakarun bisa wannan ƙoƙari tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

By ukarofi