‘Yan bindiga na samun bayanai cikin minti biyar a duk taron da muka yi – Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Katsina ya yi zargin cewa akwai ‘yan iska a cikin hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da kuma al’ummomin yankin da ke ba da bayanai ga ‘yan bindiga, ta yadda suke taimakawa ayyukan miyagun ayyuka a faɗin jihar Katsina.

Da yake magana a wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Channels da News Point Nigeria , gwamnan ya ce yaƙi da rashin tsaro a jihar na fuskantar muguwar illa daga wasu mutane da ke fallasa wasu muhimman bayanan tsaro ga ƙungiyoyin masu laifi.

Raɗɗa ya ambaci wani ɗan bindiga da ya shahara mai suna Mohammed, yana mai bayanin yadda masu ba da labari a cikin tsarin gwamnati da al’ummomi ke ba da bayanan sirri da ke taimaka wa wanda ake zargi tserewa, kamawa da kuma daƙile ayyukan tsaro.

“Wannan sanannen mutumin da ke damun mu – mun san shi, Mohammed ne, sunan sa, kowa ya san shi, Amma matsalar da muke da ita itace al’umma. Al’umma ba sa bayar da bayanan da suka dace. Zan iya cewa, ta wata hanya, wasu daga cikinsu suna taimaka masa,” in ji gwamnan.

“Ba wani ɓoyayyen abu bane domin yana samun bayanai, a ranar da na kira taron tsaro na musamman a nan gwamnatin jihar kan yadda za a gudanar da aiki da shawo kan lamarin, bayan mintuna biyar da kammala taron, ya riga ya san abin da muka tattauna.”

A cewar Raɗɗa, lamarin ya ƙara ta’azzara yayin da ake zargin shugaban ‘yan fashin na dogaro da masu ba da labari da ke cikin cibiyoyi daban-daban don sa ido kan ayyukan tsaro.

“Akwai ‘yan iska da ke ba shi bayanai a cikinmu, a gaskiya ma, ya kirkiro wata sabuwar dabara inda yake tunzura ƙauyuka don nuna adawa da gwamnati don su matsa wa gwamnati kada ta bi shi,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi zargin cewa masu ba da labari a cikin al’ummomin da abin ya shafa kan sanar da ‘yan bindigar a duk lokacin da aka tara jami’an tsaro domin mayar da martani ga hare-haren.

“Kuma duk lokacin da aka samu labarin harin da jami’an tsaro suka kai yankin, ’yan bindigar da ke cikin al’umma za su kira su su sanar da shi cewa jami’an tsaro na zuwa da kuma hanyar da suke bi, wanda zai ba su damar yin kwanton bauna ga jami’an tsaro,” in ji Raɗɗa.

“Don haka, irin wannan halin da muke ciki ke nan. Akwai ‘yan iska a cikinmu, ƴan iska a cikin jami’an tsaro, da kuma ƴan iska a tsakanin al’ummomi.”

Da yake magana kan batun tattaunawa da ‘yan fashi, duk da adawa da ra’ayin da wasu gwamnonin suka yi, Raɗɗa ya bayyana cewa, duk da cewa shi da kansa ba ya goyon bayan tattaunawa da ƙungiyoyin masu aikata laifuka, wasu al’ummomi sun nemi a ba su izinin shiga tattaunawa da ‘yan fashin.

A cewarsa, al’ummomin da abin ya shafa sun yi imanin cewa tattaunawar za ta iya taimakawa wajen dawo da zaman lafiya bayan an ɗauki tsawon lokaci ana kai hare-hare ba isasshen kariya.

“Ni ne na fara ɗaukar matakin hana tattaunawa da ‘yan bindiga, amma da lamarin ya gagara, sai al’umma suka zo wurina suka ce, ‘Ya mai girma gwamna mun gana da wadannan mutanen, a shirye suke su ajiye makamansu, kuma mun sha wahala sosai ba tare da samun kariya daga jami’an tsaro ba, don Allah a ba mu damar tattaunawa da su idan har za a iya kawo zaman lafiya.

Raɗɗa ya bayyana cewa, a ƙarshe ya bar al’ummomin su ci gaba da tattaunawar, duk da cewa ya ki sanya hannu kai tsaye a cikin lamarin.

“Na gaya musu za su iya ci gaba, amma ba zan shiga cikin sa ba. Don haka suka ci gaba.”

Gwamnan ya bayyana cewa wasu ƙananan hukumomin da suka amince da tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindiga ba su samu labarin hare-hare sama da shekara guda ba.

“A yayin da nake magana da ku a yau, akwai wasu ƙananan hukumomi da suka shiga tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindiga, kuma sama da shekara guda ba a kai hare-hare a waɗannan wuraren ba, yanzu mun samu zaman lafiya a mafi yawan kananan hukumomin da waɗannan abubuwan suka faru a da.” Inji shi.

“Na kyale su ne saboda abin da suke so ke nan, kuma ni gwamna ne bisa ga umurnin da jama’a suka ba ni, ni wane ne zan yi watsi da abin da suke so, muddin zai iya kawo sakamakon da muke bukata? Abin da muke so shi ne zaman lafiya.”

Gwamna Radda, ya ci gaba da cewa ba zai fara tattaunawa da ‘yan fashi da kan sa ba.

Ya ƙara da cewa idan ‘yan fashin suka tunkare shi don neman zaman lafiya, zai yarda a tattauna, amma sai da ƙarfin hali maimakon rauni.

By ukarofi