2027: ADC na fuskantar ficewar mambobi bayan sauya sheƙar Obi da Kwankwaso

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Alamu na nuna cewa mambobi da dama na Jam’iyyar ADC na ci gaba da ficewa daga jam’iyyar, jim kaɗan bayan da tsoffin ’yan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, suka bar jam’iyyar tare da komawa sabuwar jam’iyyar NDC.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan sabon yanayi ya biyo bayan fitar da wasu tsare-tsare daga ƙungiyar Obedient Moɓement da kuma Kwankwasiyya, waɗanda suka bayyana hanyoyin da mabiya za su bi domin ficewa daga ADC.

A daidai wannan lokaci, magoya bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun musanta rahotannin da ke cewa ana tattaunawa domin su ma su koma jam’iyyar NDC, duk da yadda sauye-sauyen siyasa ke ƙara ƙamari bayan shigar Obi da Kwankwaso cikin sabuwar jam’iyyar.

Wannan martani na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da hasashe kan yiwuwar haɗakar ’yan adawa gabanin zaɓen shekarar 2027, inda jam’iyyar NDC ke jan hankali a matsayin wata sabuwar dandali da za ta iya zama cibiyar haɗuwar manyan ‘yan siyasa na adawa.

An rawaito cewa ana zargin akwai mu’amala a ɓoye tsakanin wasu manyan jiga-jigan ADC, wasu na kusa da Atiku Abubakar, da kuma jagororin NDC, har ma ana hasashen cewa za a iya sanar da wani muhimmin matsaya a tsakiyar mako. Sai dai waɗanda ake zargin na da hannu sun ƙaryata wannan rahoto, suna mai bayyana shi a matsayin mara tushe da kuma yaudara.

Mai ba Atiku Abubakar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin rahotannin da ke cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ko tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, na tattaunawa kan komawa NDC.

Ya jaddada cewa babu irin wannan mu’amala da ta gudana, yana mai cewa da akwai wani abu makamancin haka, da tuni ya bayyana fili a cikin sansaninsu. Haka kuma a cikin ADC, shugabannin jam’iyyar sun yi gaggawar musanta rahotannin, inda suka ce babu wata tattaunawa ko yunƙurin haɗaka da NDC a halin yanzu. Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya yi watsi da zargin gaba ɗaya, yana mai cewa ba shi da tushe balle makama.

Wannan rikici na siyasa na gudana ne a daidai lokacin da jam’iyyar NDC ke ƙara samun karɓuwa a fagen siyasa, musamman bayan shigar Obi da Kwankwaso, lamarin da ya sake fasalta tattaunawa kan yiwuwar sake tsara tsarin ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa waɗannan sauye-sauye sun sanya NDC cikin sahun jam’iyyun da ake kallo a matsayin mahadar haɗakar ‘yan adawa, duk da cewa har yanzu babu wata yarjejeniya ta hukuma da aka kammala.

Majiyoyi daga cikin ‘yan siyasa sun nuna cewa duk wata mu’amala da ake yi a yanzu na bincike ne kawai da nazari, ba wai an cimma matsayar sauya sheƙa kai tsaye ba. Ci gaban da ake gani ya nuna yadda siyasar ‘yan adawa a Nijeriya ke ƙara sauyawa da motsi, yayin da jam’iyyu da jiga-jigan siyasa ke fara shiri tun da wuri domin fafatawar zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai kasance mai zafi da gasa sosai.

By ukarofi