Otedola ya ƙaryata zargin tallafa wa matatar Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen attajirin ɗan kasuwa a Nijeriya, Femi Otedola, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa shi ne ya tallafa wa gina Matatar Man Fetur ta Dangote, yana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya tsagwaronta da aka ƙirƙira a kafafen sada zumunta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Otedola ya ce waɗanda ke yaɗa irin waɗannan rahotanni na ƙoƙarin jefa ruɗani da kuma haifar da saɓani tsakanin manyan ‘yan kasuwar Nijeriya.

Ya ce, “Rahotannin da ke cewa Femi Otedola ne ya ɗauki nauyin gina Matatar Dangote ba gaskiya ba ne ko kaɗan. Ban zuba ko kobo ɗaya ba, ba dala ɗaya ba, kuma ba naira ɗaya ba.”

Otedola ya bayyana cewa, akasin abin da ake yaɗawa, abin da ya taɓa yi kawai shi ne nuna sha’awar shiga cikin shirin sayar da hannun jari na matatar da za a yi a nan gaba.

Ya ƙara da cewa, labarin gaskiya da ake ɓoye shi ne cewa yana neman samun wani kaso na musamman domin shiga cikin wannan shirin na sayar da hannun jari.

Haka kuma, ɗan kasuwar ya ƙaryata zargin da ke cewa shugaban bankin United Bank for Africa (UBA), Tony Elumelu, da shugaban kamfanin Globacom, Mike Adenuga, sun taimaka wajen ɗaukar nauyin aikin.

A cewarsa, Alhaji Aliko Dangote bai taɓa neman kuɗin tallafi daga gare shi ko sauran ‘yan kasuwar ba, yana mai bayyana irin wannan zargi a matsayin yunƙurin ƙirƙirar rarrabuwar kai tsakanin shugabannin ɓangaren masu zaman kansu.

Ya ce: “Zan iya tabbatar da cewa a kowane lokaci Dangote bai nemi kuɗi daga Elumelu ko Adenuga ko ni ba. Kamfanin Dangote ƙungiya ce mai tsari da ta kware wajen samar da jari ta hanyoyi na doka da tsari.”

Otedola ya bayyana rahotannin a matsayin wata dabara da aka shirya domin haifar da sabani a tsakanin ‘yan kasuwar ƙasar, yana mai cewa waɗannan mutane sun gina manyan harkoki, sun samar da ayyukan yi, kuma sun zuba jari a Nijeriya tsawon shekaru, don haka ba su cancanci a yi amfani da sunayensu wajen yaɗa aage ba.

Ya kuma yi kira ga masu yaɗa irin waɗannan labarai da su daina, yana mai cewa Nijeriya na buƙatar gaskiya ba ƙarya da ake kawatawa da sunan bayanan sirri ba.

Martanin Otedola na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rukunin kamfanonin Dangote ya ƙaryata wani saƙo da aka wallafa a shafin ɗ, inda aka yi iƙirarin cewa Dangote ya taɓa neman kuɗi daga abokai domin ci gaba da aikin matatar a shekarar 2021.

Kamfanin Dangote ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne a ce an gina Matatar Man Fetur da sinadarai ta Dangote da rancen kuɗi daga abokai, yana mai jaddada cewa shugaban kamfanin ba ya amfani da irin wannan hanya wajen samar da kuɗin gudanar da ayyukansa.

By ukarofi