An tsinci gawar ɗan jami’ar tarayya bayan zargin halaka kansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An gano wata gawar wani ɗalibin aji ɗaya na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure mai suna Favour Olaniyi a bayan gari ta yankin ƙofar arewa ta jami’ar.

Mamacin, wanda ɗan tsangayar nazarin taswira ne a jami’ar, ganin gawar tasa ya sa aka fara zargin yiwuwar ya halaka kansa ne.

Haka kuma, an ga wata kwalbar maganin kashe ƙwari a gona a kusa da inda aka samu gawar.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar ta FUTA, Adegbenro Adebanjo ya koka game da rashin ɗalibin, inda ya ce tuni aka sanar da iyayen marigayin.

Ya ce, an samu gawar ne a kusa da gidan wajen makaranta da ɗalibin yake zama.

Tuni dai aka baza jami’an tsaro da na jami’ar zuwa wajen da aka tsince mataccen ɗalibin, inda suka ɗauke gasar zuwa wajen adana gawarwaki.

By Babaji