An yaba wa Dikko Raɗɗa kan cigaba da biyan giratuti ga ma’aikatan ƙananan hukumomi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An yaba wa Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa kan cigaba da biyan giratuti ga ma’aikatan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar Katsina.

Tsohon shugabana ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa reshen jihar Katsina kwamred Mannir Suleiman yayi wannan yabo a hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce wannan ƙoƙari da Gwamnan yayi ya nuna tausayawa da ƙauna da yake wa ma’aikatan gwamnatin jihar baki ɗaya.

Kwamred Suleiman Wanda shine shugaban ƙungiyar cigaban Funtua ya bayyana cewa yanzu haka tsaffin ma’aikatan ƙananan hukumomi na cike da farin ciki da annashuwa domin wannan mataki zai taimaka masu su tanaji kayan noma ganin damuna ta sauka.

Ya kuma yaba wa gwamnan kan yadda ya fito da shirye shirye na inganta rayuwar ma’aikata a jihar.

Ya bayyana tsarin sayar da kayan masarufi ƙarƙashin shirin Rumbun Sauƙi da sayawa malaman makarantun firamare a karkara da babura masu amfani da hasken rana da sauran su.

Kwamred Suleiman ya yi kira ga gwamnan ya duba yiwuwar fitowa da tsare tsare na tallafawa ma’aikatan da suka ajiye aiki domin a cewar sa yawancin su na cikin damuwa

By ukarofi