Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata ya jagoranci tawaga zuwa taron ƙasashen Afirka da ƙasar Faransa (Africa Forward Summit) wanda aka yi a babban ɗakin taro da ke Nairobi a ƙasar Kenya.
Shugaba Tinubu ya nemi a yi sauye-sauye ta fuskar tsarin hada-hadar kuɗi ta duniyar da ƙarfafa tattalin arziƙin Afirka ta hanyar mai da hankali ga bunƙasar masana’antu da yalwar arziƙi.
Taron ƙasashen Afirka da Faransa an gudanar da shi ne bisa jagorancin Emmanuel Macron da William Ruto da kuma ya ƙunshi shugabannin ƙasashe sama da 30. Antonio Guterres, shugaban majalisar ɗinkin duniya da Mahamoud Youssouf, shugaban ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ne suka gabatar da jawabin buɗe taro.
A nasa ɓangaren, Shugaba Tinubu, a gefen taron, ya gana da shugaban ƙasar Madagascar, Michael Randrianirina; da shugaban hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afirka, Patrice Motsepe, inda suka tattauna kan burin Nijeriya na ɗaukar nauyin ba da kyaututtuka na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2026.
A yayin da yake magana a wurin taron, shugaba Tinubu ya fito da irin albarkar da Nijeriya ke da ita a ɓangaren tattalin arziƙi da ya shafi teku, yana mai alƙawarin ba da haɗin kai a ɓangaren tsaron teku ta hanyar shirin samar da abubuwan more rayuwa da suka shafi teku.
“A yau, na yi magana a fili kan cewa Nijeriya za ta ƙarfafa haɗin kai ta hanyar shirinmu na tattalin arziƙi na teku da tattara bayanan sirri wanda za ta bai wa ƙasashen yankin gaɓar tekun Guinea,” ya faɗa, inda ya ƙara da cewa lallai ne a samu tsarin haɗaka ta fuskar dokoki da jami’an tsaro a yankin bakiɗaya.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa akwai buƙatar samar da hanyar zuba jari mai zaman kansa ta hanyar samar da tsaro a kan hanyoyin da ake bi ta teku da dokoki da tsarin shari’a. Ya kuma ce Nijeriya za ta ci gaba ɗaukar matakan kula da yanayi dai dai da tanadin tashoshin ruwa na zamani da sauye-sauye na dijital da ake amfani da suu wajen harkokin ruwa.
“Bayan mara wa Nairobi baya, Nijeriya ta jadadda cewa ‘yancin gudanar da harkokin ruwa da kula da tekuna abu ne da ya wajaba domin kawo sauyi a fannin tattalin arziƙi na teku,” in ji shugaba Tinubu, inda ya buƙaci ƙasashen Afirka da su matsa daga “dogaro zuwa samun ‘yancin tafi da harkokin teku.”
A gaba da sha’anin kuɗi na duniya, shugaba Tinubu ya sabunta kiransa na kawo gyara kan abin da ya kira da rashin adalci wajen hada-hadar kuɗi a duniya wanda ke zama tarnaƙi ga cigaban masana’antu a Afirka.
“Duk da shafe shakaru da samun ‘yancin kai, Afirka na samin kaso 2% na ɗaukacin kayayyakin da ake samarwa,” ya faɗa, yana mai cewa nahiyar na ci gaba da fitar da albarkatunta zuwa ƙasashen waje da shigo da kayayyakin da aka sarrafa a farashi mai tsada saboda tsare-tsaren kuɗi wanda ke kawo cikas ga cigaban masana’antun Afirka.
Shugaban ƙasa ya ce, sauye-sauyen da Nijeriya ta ɓullo da su na baya-bayan nan sun haɗa da cire tallafin man fetur da samar da tsayayyen farashin canjin kuɗi da bunƙasa ƙarfin jarin bankuna wanda ya haura Dala biliyan 3.4 da ficewa daga jerin ƙasashen da ake safarar haramtattun kuɗi waɗanda duka matakai ne da aka ɗauka domin ƙarfafa guiwar masu zuba hannun jari da inganta asusun ajiyar Nijeriya na ƙasasshen waje zuwa Dala 45.5 da rage yawan bashin Nijeriya idan aka kwatanta da tattalin arziƙi a ma’aunin GDP wanda zai kai kaso 32.3% a 2026.
Sai dai ya ce, Nijeriya za ta kashe kusan Dala biliyan 11.6 wajen biyan bashi a 2026, inda ya bayyana cewa yawan kuɗin da ta kashewa wajen biyan bashi da zama babban tarnaƙi na ci gaban masana’antu.
“Kowanne Dala ɗaya da ta fice daga asusunmu domin biyan kuɗin ruwa, kuɗi ne da ba wai tafiya yake ɓangaren samar da ƙarafa ba ko ɓangaren tufafi ko sarrafa kayan amfanin gona ko masana’antu,” inji Tinubu.
Ya kuma ce masu masana’antu a Afirka ba za su iya yin gogayya da takwarorinsu na duniya ba idan har za a ce tsadar biyan bashi ya ninka sau biyar idan aka kwatanta da takwarorinsu na Turai da Asiya da Arewacin Amurka, yana mai cewa tsarin hada-hadar kuɗi da “wata hanya ta rushe masana’antu a Afirka.”
“Nijeriya ba bara take yi ba,” ya faɗa. “Muna neman a samar da tsarin kuɗi ne na duniya domin bai wa Afirka damar bunƙasa masana’antunta.”
A game da batun masu balaguro, shugaba Tinubu ya ce za a iya rage wannan matsala ce ta hanyar magance talauci da rashin aikin yi da matsalar tsaro a ƙasashen da ke yankin. Ya buƙaci abokan haɗin kai wajen samar da ci gaba da su tallafa wajen zuba hannun jari kan sauyin yanayi da samar da makamashi da samun ƙwarewa a fannin dijital da samar da ayyukan yi.
“Mutanen da suke da aiki yi da tsaro da kyakkyawan fata a ƙasashensu ba za su yi kasada da rayuwarsu a bayan ƙatuwar motar da aka yi safararsu ba,” ya faɗa.
Shugaba Tinubu ya yi kira da a samu kyakkyawan tsari wajen tafi da masu tafiya ci-rani, inda ya goyi bayan tsarin kula da ‘yan gudun hijira na ƙungiyar ƙasashen Afirka. Sai dai ya nemi a samu haɗin kai tsakanin hukumomi na gida da na ƙasashen duniya.
A cikin tawagar Nijeriya akwai manyan ‘yan kasuwa kamar Aliko Dangote, Tony Elumelu da Abdulsamad Rabiu. Sannan ministoci sun gudanar da taruka da shiga tattaunawa kan kasuwanci, ƙirƙirarriyar basira da fasahhar zamani, kasuwanci da masana’antun sarrafa kyayyakin gona, lafiya, sauyin yanayi, da makomar masana’antu a Afirka a ƙarƙashin tsarin kasuwanci ba tare da shinge ba na Afirka.
