Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar haɗin kan arewacin Nijeriya da zaman lafiya da bunƙasa, wato Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative (ACI) ta nuna rashin jin daɗinta kan rikicin shugabanci da ke addabar ƙungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), tana mai bayyana lamarin a matsayin abin kunya da ya jefa Arewacin Nijeriya cikin ba’a da raini a idon jama’a.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Dr. Abdullahi Idris, ya aikewa da manema labarai, ACI ta bayyana damuwarta kan yadda rikice-rikice, zarge-zarge da rarrabuwar kai suka yi ƙamari a cikin ACF.
Kungiyar ta ce rikicin ya sa ACF ta rasa mutunci da martabar da ake tsammani daga babbar ƙungiyar da ke wakiltar muradun Arewa.
ACI ta ce musayar sanarwa da martani, zarge-zargen karya kundin tsarin mulki, almundahanar kuɗi, amfani da ofis ba daidai ba, da kuma batun shiga ‘yan sanda cikin rikicin sun mayar da ACF abin kallo da abin kunya a bainar jama’a.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan rikici na faruwa ne a lokacin da Arewa ke fama da matsaloli masu tarin yawa kamar rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, ƙarancin ilimi, matsin tattalin arziki da kuma raunin haɗin kai tsakanin al’umma.
“Abubuwan da ke faruwa dangane da rikicin shugabancin ACF sun zama babban abin kunya ga Arewa da al’ummarta,” inji sanarwar.
ACI ta ƙara da cewa maimakon ACF ta kasance ginshiƙin haɗin kai da jagoranci mai ma’ana ga yankin Arewa, rikicin ya nuna rarrabuwar kai, ruɗani da gazawar shugabanci a idon sauran sassan ƙasar nan.
Kungiyar ta jaddada cewa babu wani yanki da zai samu ci gaba idan aka bar son rai, rikicin iko da anfani na ƙashin kai su rinjayi muradin jama’a da ci gaban bai ɗaya.
Saboda haka, ta buƙaci dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin da su fifita muradin Arewa fiye da buƙatun kansu, tare da rungumar tattaunawa, haƙuri da bin doka domin kare mutuncin yankin.
Haka kuma, ACI ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da inganta zaman lafiya, haɗin kai, riƙon amana da shugabanci nagari a faɗin Arewacin Nijeriya.
Dr. Idris ya ce ƙungiyar ta ƙunshi masu hangen nesa da jajircewa wajen yi wa yankin hidima cikin gaskiya da kishin ci gaba.
Ya ce ACI za ta ci gaba da bayar da gudunmawa kan muhimman batutuwan da suka shafi Arewa, musamman ta fuskar tsaro, bunƙasa matasa, ilimi, tattalin arziki, zaman lafiya da haɗin kai.
“Arewacin Nijeriya na buƙatar shugabanci mai nagarta da hangen nesa domin tunkarar matsalolin da yankin ke fuskanta. Wannan ba lokaci ba ne na rikice-rikice da abin kunya a bainar jama’a,” inji shi.
Daga ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga dattawan Arewa, ‘yan siyasa, sarakuna, ƙwararru da ƙungiyoyin farar hula da su haɗa kai wajen dawo da martabar Arewa tare da samar da shugabanci nagari da zai samu girmamawa a faɗin ƙasa.
