Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta soji a Arewa maso Gabas, wato Operation HADIN KAI, sun sanar da ci gaba da samun nasarori a hare-haren da suke kai wa ’yan ta’adda ƙarƙashin atisayen Operation DESERT SANITY, inda suka ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su tare da kama waɗanda ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar 13 ga Mayu, 2026, ya bayyana cewa dakarun sun samu nasarar ceto mata da yara shida da aka sace bayan wani samame da suka kai kusa da tsaunukan Mandara.
Rahoton ya ce, sojojin sun gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri sakamakon wani farmakin sama da aka kai yankin, inda suka kai samame a wata hanyar da ake zargin ’yan ta’adda ke amfani da ita a kusa da Amuda a ranar 12 ga Mayu, 2026.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da Aisha Musa mai shekaru 18, Aisha Mohammed mai shekaru 17, Fatima Yahaya mai shekaru 20, Saudatu Musa mai shekaru 4, Garba Mohammed mai shekaru 5 da kuma Mohammed Yahaya ɗan wata uku.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da aka ceton na daga cikin mazauna garin Ngoshe da mayaƙan Boko Haram da ISWAP suka sace yayin harin da suka kai yankin a ranar 3 ga Maris, 2026.
Bayan ceto su, an kai su wani asibitin soji domin kula da lafiyarsu kafin daga bisani a miƙa su ga iyalansu ta hannun shugaban al’ummar Ngoshe, Malam Adamu Gunda.
A wani samame daban da aka gudanar a wannan rana, dakarun Operation HADIN KAI da ke sansanin Tango 7 a ƙaramar hukumar Konduga sun kama wata mata mai suna Hauwa Bulama mai shekaru 40 da ake zargin tana da alaƙa da ’yan ta’adda.
An ce jami’an sun samu kayan amfani irin su sabulai, fitila da kayan ɗanɗano a hannunta. Binciken farko ya nuna cewa matar na kan hanyarta ta zuwa Gezuwa domin haɗuwa da ’ya’yanta huɗu da ake zargin suna cikin ƙungiyar ’yan ta’adda.
Haka kuma, bisa bayanan sirri da aka samu daga binciken da ake yi tare da saƙonnin sadarwa da aka cafke, dakarun rundunar a Sashi na 2 tare da haɗin gwiwar jami’an leƙen asirin soji sun kama wasu mutane biyu a Damaturu, jihar Yobe.
An bayyana sunayensu da Bakura mai shekaru 18 da Adiza mai shekaru 17. Kama su na da alaƙa da wani wanda ake zargin dillalin harsasai ne mai suna Ba’akaka Abubakar, wanda aka fi sani da Modogol, da aka kama yana ƙoƙarin kai wa ’yan ta’adda harsasai.
Binciken farko ya nuna cewa an bai wa Adiza aikin karvo harsasan daga hannun wanda aka kama domin kai wa wani kwamandan ’yan ta’adda.
A yanzu haka ana tsare da waɗanda ake zargin yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da farautar sauran wasanda ke da hannu a lamarin tare da ƙoƙarin ƙwato harsasan da ake son kai wa ’yan ta’addan.
Rundunar haɗin gwiwar ta tabbatar wa al’umma cewa za ta ci gaba da ƙara ƙaimi wajen rusa sansanonin ’yan ta’adda, ceto mutanen da aka sace da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.
Babban hafsan rundunar sojin ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewa da jajircewar da suke nunawa a bakin aiki, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da kai irin waɗannan nasarori.
