Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Gombe
Ƙungiyar da’awa da agaji ta Jihar Gombe ta bayyana cewa ta tallafawa sama da marayu da zawarawa 2,000 da aka yi wa rajista, tare da yin kira ga masu hannu da shuni, hukumomin gwamnati da sauran masu faɗa a ji da su taimaka wajen ci gaba da faɗaɗa shirye-shiryenta na jin ƙai.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Muhammad Lawan ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ƙungiyar da ke Gombe.
Dakta Lawan ya ce ƙungiyar na ci gaba da jajircewa wajen yaɗa addini da gudanar da ayyukan jin ƙai, musamman ta hanyar tallafa wa marasa galihu, musamman marayu da zawarawa da suke dogaro da taimakon ƙungiyar domin rayuwa.
Ya bayyana cewa ƙungiyar na bayar da tallafi akai-akai da suka hada da kayan abinci, tufafi da sauran kayan agaji, musamman a lokutan watan Ramadan, bukukuwan Sallah da sauran lokutan matsin rayuwa.
A cewarsa, ƙungiyar da’awa da agaji tana kuma gudanar da shirye-shiryen ilimi da faɗakarwa ta hannun kwamitin ilimi, wanda ke shirya taruka da bitoci domin yaɗa koyarwar addinin Musulunci da inganta tarbiyya a cikin al’umma.
Ya ƙara da cewa ɓangaren Hisbah na kungiyar na taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsafta yayin tarukan addini da bukukuwan al’umma, lamarin da ke taimakawa wajen samar da haɗin kai da zaman lafiya a jihar.
Sai dai Dakta Lawan ya nuna damuwa kan wasu ƙalubalen da ke kawo cikas ga ayyukan ƙungiyar, ciki har da rashin wadatattun ɗakunan kwanan ɗalibai a makarantu da kuma lalacewar motocin ƙungiyar guda biyu da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan wayar da kai da kai ɗauki.
Ya ce matsalolin sufuri da kayan aiki sun rage wa ƙungiyar damar kaiwa ga karin mabuƙata da faɗaɗa ayyukan agajin da take gudanarwa.
Saboda haka, shugaban ƙungiyar ya yi kira ga daidaikun mutane, ƙungiyoyin agaji da hukumomin da abin ya shafa da su ƙara bai wa ƙungiyar goyon baya, yana mai cewa ɗorewar tallafi zai ba ƙungiyar damar ci gaba da kula da yawan marayu da zawarawa da ke ƙarƙashin shirye-shiryenta a fadin Jihar Gombe.
