
Rundunar ‘yan sanda ta shigar da malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Adam Zubair Adam da aka fi sani da Baffa Hotoro, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin sa da amfani da kafafen sada zumunta wajen yin kalaman ɓatanci akan marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da Sheikh Mannir Adam Koza.
Rahotanni sun bayyana cewa, takardun kotu sun nuna cewa Hotoro ya yi wasu wa’azozi a TikTok da Facebook inda ake zargin ya kira malaman biyu da “Mushrikai” tare da cewa ba a yarda su shiga Ka’aba ba.
‘Yan sanda sun bayyana cewa irin waɗannan kalamai na iya haddasa rikicin addini da tayar da zaune tsaye tsakanin mabiya ɗarikar Tijjaniyya.
Rahotanni sun ce an shirya gurfanar da malamin a ranar 11 ga Mayu, 2026, amma bai bayyana a kotu ba duk da cewa an tabbatar da an aika masa da sammaci.
Tun farko dai jami’an tsaro sun taɓa kama shi a shekarar 2023 bayan koke-koken da aka shigar kan kalamansa, kafin daga baya a sake kama shi a watan Fabrairun bana bayan sababbin ƙorafe-ƙorafe daga iyalan Sheikh Dahiru Bauchi da Sheikh Koza.
Wasu malamai da lauyoyi sun bayyana shari’ar a matsayin muhimmiyar hanya ta rage kalaman tunzura jama’a a wa’azi da tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabiya addini. Sun yabawa masu ƙarar kan bin hanyar doka maimakon ɗaukar matakin ramuwar gayya.
