“Ni ƙwararriya ce musamman a fannin haƙƙin mata”
Daga JOHN D. WADA a Keffi
Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ita ce shugabar Jami’ar Gwamnatin Jihar Nasarawa da ke garin Keffi. Kwararriya ce a fannin ilimin addinin Islama kuma mace ta farko da aka taɓa naɗa wa a muƙamin shugabar jami’ar jihar bakiɗaya.
A tattaunawar musamman da Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Nasarawa, JOHN D. WADA, ya yi da ita a ofishinta da ke jami’ar a garin Keffi ya gano cewa, farfesar a yanzu haka tafi kowacce mace a jihar ta Nasarawa samun lamboyin yabo daga ciki da wajen ƙasar nan bakiɗaya sakamakon gagaruman gudunmawa da ta ke bayarwa a kullum wajen bunƙasar harkokin ilimin zamani da na addini da sauransu. Farfesa Sa’adatu ta kuma shawarci ’yan uwanta mata da su tashi su nemi ilimi ko su kama sana’a, don tallafa wa iyalansu da sauransu. Ga dai yadda hirar ta kasance:
MANHAJA: Da farko masu karatu za su so su san wacce ce farfesa Sa’adatu Hassan Liman ko da a takaice ne?
FARFESA SA’ADATU: To Assalamu alaikum. A taƙaice dai tarihina shi ne kamar haka: Kamar yadda ka sani sunana farfesa Sa’adatu Hassan liman. Ni ce shugabar wannan babbar jami’armu ta gwamnatin jihar nan ta Nasarawa.
Ni ƙwararriya ce a fannin ilimin Islamiya a shashin karatun Islamiyar da bunƙasa na fannin zamantakewa na babbar jami’ar nan da ke nan garin Keffi hedikwatar ƙaramar Hukumar Keffi, wato ina nufin ni farfesa ce a fannin.
Kuma har ila yau ni ƙwararriya ce musamman a fannin haƙƙin mata da bil’adam bakiɗaya da sauransu.
Bayan karatun firamari da na sakandare da sauransu na samu digiri ɗina na farko a shekarar 1998 a jami’ar Jos da ke Jihar Filato inda da ikon Allah na kuma cimma matsayi da ya dace in zama cikakkiyar farfesar ilimin Islamiya ta jami’ar nan, wato a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 2017 kenan.
Ina da aure da ‘ya’ya kamar yadda ka sani da dakta Hassan Liman da ke da sarautar wakilin Lafiya kuma babban lauya ne mai zaman kansa wato SAN a turance daga jihar nan kamar yadda ni ma daga jihar nan ce wato daga nan ƙaramar Hukumar Keffi, a taƙaice kenan.
To ko za ki bayyana mana wasu daga cikin muƙamai da kika riƙe daga lokacin da kika kammala karatunki zuwa yanzu musamman a jami’ar nan?
Daganan dai da yardar Allah sai na fara riƙe wasu muƙamin fannin ilimin dana gudanarwa da dama a babbar jami’ar nan da suka haɗa da; muƙaddasiyar shugabar fannin harkokin ɗalibai wato daga shekarar 2010 zuwa 2012 sai mataimakiyar shugaban wannan fannin harkokin ɗaliban a watan Fabrelun shekarar 2013.
Daganan sai shugabar riƙo ta fannin karatun addini daga watan Afrulun shekarar 2013 zuwa watan Maris na shekarar 2014.
Sai shugabar riƙon ƙwarya ta sashin karatun Islamiya daga watan Maris na shekarar 2013 zuwa watan Oktobar shekarar 2014.
Sai mataimakiyar shugabar fannin harkokin ɗalibai daga watan Mayun shekarar 2014 zuwa watan Oktobar shekarar 2014.
Daga watan Oktobar shekarar 2016 da ikon Allah na kuma riƙe muƙamin mataimakiyar shugaban jami’ar nan (ɓc) a fannin ilimi a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban jami’ar nan wato farfesa Muhammed Akaro Mainoma.
Har ila yau na kuma yi aiki a matsayin daraktan neman bayyanai (Research) da yaɗawa na jami’ar nan daga shekarar 2019 zuwa 2021.
Daganan nan dai sai tsohon shugaban jami’ar nan na baya-bayan nan wato farfesa Suleiman Bala Mohammed ya naɗa ni a matsayin mataimakiyar sa a fannin gudanarwa (Administration) wato daga watan Afrilun shekarar 2021 zuwa watan Yulin shekarar 2023 kenan wanda shi ne yakasance babban muƙamin da na riƙe na ƙarshe kafin da ikon Allah muƙamin da nake riƙe da shi yanzu na sabuwar shugabar jami’ar nan kuma mace ta farko da ta riƙe mukamin a tarihin jami’ar.
Kaji wannan shi ma a taƙaitaccen kenan kamar yadda ka yi tambaya don tabbas kamar yadda ka sani wannan taƙaitaccen tarihi na ne da ayyukana, ban bayyana maka dukka ba.
To masu karatu za su so su san ko bayan waɗannan muƙamai da kika riƙe a fannin ilimin zamani ko da wasu da kika riƙe a wajen ilimin?
Tabbas bayan muƙaman fannin ilimin na kuma riƙe wasu a fannonin rayuwa daban-daban da suka haɗa da, shugabar malaman koyarwar Arabiya ta Islamiya inda na kuma riƙe wasu mahimman muƙaman cibiyoyi da ƙungiyoyin ilimi da ke zaman kansu kamar ƙungiyar Dukka Malaman Karatun Arabiya da Islamiya ta Najeriya bakiɗaya ni kuma mamba ce ta Cibiyar Kwararru a Fannin Kuɗi da Tattalin Arziki na Najeriya (FIIFPN) da mambar Cibiyar Bincike da Bunkasa (IRDI) da mambar Cibiyar Masu Harkokin Ilimi ta Amurka (ACLS) da mambar Cibiyar Ilimin Addini ta Amurka (ARR) da ke Atalanta Georgia da dai sauran su da dama da lokaci bazai bari in bayyana maka duka ba.
Ko farfesa za ta bayyana mana wasu lambobin yabo da ta samu kawo yanzu sakamakon waɗannan gudunmawa da sadaukarwa da kike yi wa al’ummar ta fannin ilimin?
A gaskiya ba wai yabon kai ko wani abu kamar haka ba zan iya cewa da yardar Allah kawo yanzu na samu wasu lambobin yabo wato awards kenan a turance daga wasu mahimman cibiyoyi da ƙungiyoyi da dama daga ciki da wajen ƙasar nan bakiɗaya waɗanda suke bibiyan ire-iren gudunmawa da nake bayarwa a fannin ilimi da sauran fannonin rayuwa inda suka bani lambobin yabon kamar ta jagorar cibiyar ƙwararru a fannin kuɗi ta Islamiya a Najeriya bakiɗaya (FIIFPN) da lambar yabo ta Ambasadar zamantakewa da zaman lafiya ta cibiyar UFUK wadda aka bani a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2022 da wata lambar yabo ta musamman daga gidauniyar shugabanni ta Sir Ahmadu Bello da satificate na ƙwarewa wadda cibiyar matasan Arewacin ƙasar nan ta Sir Ahmadu Bello (ABYCN) ta ba ni da taurariyar adalci da bunƙasar ilimi ta shekarar 2021 da sauransu da dama da shi ma bazan iya bayyana maka duka a yanzu ba.
Sai dai zan iya tunawa na kuma lashe gasar karatu ta malamai ta shekarar 2020 wadda cibiyar Stantall Africa Initiatiɓe (STAI) ta Najeriya ta shirya a watan Oktobar shekarar 2020 da lambar yabo ta musamman daga ƙungiyar mata a kwalejin ilimi (WICE) dangane da gudunmawa da nake bayarwa wajen ɗaukaka tare da bunƙasa harkokin ilimi bakiɗaya musamman tsakanin mata ‘yan uwana.
An kuma karrama ni da lambar yabon ƙwararru na musamman a fannin bincike ta musamman dangane da tallafa wa mata don zaman lafiya da karatun jinsi daga cibiyoyin UNESCO da SUZANNE da Mubaraka-Japan wadda aka bani da ƙasar Masar a shekarar 2006 da sauran su.
Ka ji wannan shi ma a taƙaice kenan.
To a ƙarshe saboda ƙaramcin lokaci kamar yadda kika roƙa kada mu cinye miki lokacin a matsayin ki ta shugaba kuma mace, wacce shawara kike da ita ga musamman ga ‘yan uwanki mata?
A gaskiya shawarar da nake ba kowa musamman mata a wannan zamani a kuma kullum ita ce, su tashi su nemi ilimin zamani dana addini don su ne ginshiƙin zaman duniya.
Sai da ilimi mace zata iya yin komai ko ta kai duk wani matsayi da take buƙata a rayuwa, don har bautan Allah ma sai mutum yana da ilimi yasan dokokin Allah kafin ya iya kiyayewa da sauran su.
Sa’anan idan mace ba ta samu damar karatu ba to ta kama sana’a komai ƙankantar ta don lokaci ya wuce da mace zata riƙa dogara ga mijinta kaɗai.
Yakamata a wannan mawuyacin hali ace mace tana yin sana’a tana kuma tallafa wa mijinta ne wajen ɗawainiyar iyalanta da sauransu maimakon ta zauna sai maigidanta ya kawo mata komai.
Duk matsayi da wasun mu muka tsinci kanmu yau da yardar Allah ne da kuma jajircewar mu ta neman ilimin addini da na zamani ba kawai haka ba ne.
Mu kuma riƙe addini a duk harkokinmu na yau da kullum, mu riƙa kiyaye dokokin Allah a kodayaushe.
Saboda haka a taƙaice shawarar kenan da nake da ita ga mata ‘yan uwana, a tashi a nemi ilimin addini da na zamani. Wacce ba ta da damar yin haka to ta kama sana’a don rufin asirin ta da na iyalanta bakiɗaya.
