Ɗan Majalisar Wakilai mai ci na hannun daman Akume ya faɗi a zaɓen fidda gwanin APC a Benuwai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Lahadi Kwamitin Majalisar Dokoki ta Ƙasa akan shirya zaɓen fidda gwani a Jihar Benuwai, ya sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar a mazaɓun tarayya guda 11 na jihar.

Acikin 10 na ‘yan majalisa masu ci da suka shiga takarar, guda huɗu sun yi nasara a mazaɓunsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da Ojotu Ojeme na mazaɓar tarayya ta Apa/Agatu Cif Regina Akume ta Gboko/Tarka, Blessing Onuh ta Otukpo/Ohimini, da kuma Solomon Wombo na Katsina-Ala/Logo/Ukum.

Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Ado/Okpokwu/Ogbadibo, Philip Agbese, ya koma jam’iyyar LP da fari domin sake zaɓar sa a ƙarƙashinta.

Haka kuma, ‘yan majalisa da dama na hannun daman Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume sun rasa damar koma wa kujerunsu yayin zaɓen.

Waɗanda abin ya shafa sune Terseer Ugbor na Kwande/Ushongo, Sesoo Ikpagher na Konshisha/Vandeikya, Asema Achado na Gwer ta Gabas/Gwer ta Yamma, Sekav Iortyom na Buruku, da kuma Dickson Tarkighir na Makurdi/Guma, da dai sauransu.

Baya ga Cif Regina Akume, wadda matara Akume ce, da dama daga cikin ‘yan majalisar da suka yi nasara ana ɗaukar su a matsayin masu biyayya ga Gwamna Hyacinth Alia na jihar, kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito.

By Babaji