Tsagin PDP zai tantance Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a Talata

Spread the love

Tsagin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ya bayyana cewa zai tantance tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa shi kaɗai a ranar Talata mai zuwa.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Lahadi, ta ce za a gudanar da tantancewar masu neman tikitin takara da misalin ƙarfe 10 na safe gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran tantance masu neman takarar kujerun majalisun dokokin jihohi 2,122, na majalisar wakilai 748, sanatoci 198, gwamnoni 112 da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, ko da yake jam’iyyar ba ta bayyana sunan ɗan takarar shugaban ƙasar ba, wata majiya daga cikin PDP ta tabbatar wa jaridar cewa Jonathan ne kaɗai zai shiga tantancewar.

Kwamitin tantancewar mai mambobi 14 ya haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo, tsohon gwamnan Filato Jonah Jang, da tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Tom Ikimi.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Olabode George, Babangida Aliyu, Maryam Ciroma, Zainab Maina, Josephine Anenih, Abdul Bulama, Esther Uduehi, Tony Aziegbemi, Sunday Solari da Anicho Okoro wanda zai kasance sakataren gudanarwa na kwamitin.

Jam’iyyar ta ce kwamitin ya samu amincewar kwamitin zartarwa na ƙasa na PDP a taronsa na 104.

Sanarwar ta ƙara da cewa matakin na cikin jadawalin shirye-shiryen jam’iyyar domin babban zaɓen shekarar 2027.

A baya dai, wasu matasa ƙarƙashin ƙungiyar Coalition for Goodluck Jonathan sun gudanar da gangamin goyon baya a gidan Jonathan da ke Abuja ranar 7 ga watan Mayu, inda suka buƙace shi da ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Sai dai tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai tuntubi jama’a da masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci kan matakin da zai ɗauka.

By Babaji