Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta amince da horar da masu sana’a 74 kan ƙirƙira da haɓaka samfurin motocin lantarki (Electric Vehicle – EV), a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa matasa da bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire na fasaha a jihar.
Mai kula da cibiyar koyon sana’o’i (Katsina Youth Craft Village), a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa shirin horaswar na tsawon watanni shida za a gudanar da shi ne a cibiyar, tare da haɗin gwiwar kamfanin Maglush Electric Vehicle, wani kamfanin EV na cikin gida mallakin ‘yan asalin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa an tsara shirin ne domin bai wa matasa masu sana’a ƙwarewar zamani a fannin fasahar motocin lantarki, tare da shirya su don cin gajiyar damar da ke kunno kai a ɓangaren sufuri mai amfani da makamashi mai tsafta.
Mai kula da cibiyar ya ce za a ɗauki mahalarta horon daga dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar domin tabbatar da samuwar ƙwararrun masu gyara da kula da motocin lantarki a faɗin Katsina.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen tallafa wa shirin gwamnatin jihar na rarraba baburan lantarki ga malamai, ta hanyar samar da ƙwararrun ma’aikatan da za su riƙa kula da su da gyaransu.
Haka kuma, an nuna cewa haɗin gwiwar zai haɗa da tsarin canja wurin fasaha (technology transfer) domin bai wa Katsina Youth Craft Village damar ci gaba da gudanar da irin waɗannan shirye-shiryen horaswa na EV a nan gaba ba tare da dogaro da waje ba.
Mai kula da cibiyar ya bayyana wannan amincewa a matsayin wata alama ta jajircewar Gwamna Raɗɗa wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, ci gaban matasa, da kuma ingantaccen ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa a Jihar Katsina.
