Masarautar Katsina ta bayar da lambobin yabo ga hakimai da su ka yi zarra a hawan ƙaramar sallah

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya gabatar da kofin da lambobin yabo ga hakimai da su kayi zarra a hawan ƙaramar sallah da ta gabata.

Magajin Garin Katsina, Alh. Aminu Abdulmumini Kabir Usman shine ya zamo na ɗaya a hawan sallah ƙarama da ta gabata, inda Ƙauran Katsina Alh. Aminu Nuhu Abdulƙadir ya zamo na biyu sai Ɗan Galadiman Katsina Hakimin Ƙafur yazo na uku.

Kurayen Katsina Alhaji Darda’u shine yazo na huɗu sannan daga na huɗu zuwa na goma an basu lambar yabo sannan sauran hakiman su 28 su ma an basu takardar yabon domin a ƙara ƙarfafa masu gwiwa domin su ƙara yin ƙokari.

Da yake gabatar da jawabin bayan Kammala bada kyaututtukan Mai Martaba Sarkin Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bayyana dalilin da yasa aka ƙirƙiri wani kwamitin wanda zai sa ido akan hawan sallah domin ƙara tsabtace shi tare da ingantashi ta yadda kowa zai yi sha’awa.

Kwamitin na wucin gadi ne sai dai sarkin ya mai da shi na dindindin tare da basu ofishin da za su gudanar da aikin su.

Kwamitin kula da hawan sallah wanda Galadiman Katsina Mai Sharia Sadiq Abdullahi Mahuta ke jagoranta tare da shi akwai Sardaunan Katsina Ahamad Rufai Sai Marafan Katsina.

Ya bayyana irin abubuwan da kwamitin ke kula da su wajen zaƙulo waɗanda suka yi nasara, ta hanyar tsara tawagar su wajen kwalliyar da Iya hawa doki ba tare da cinkoso ba.

Mai Martaba Sarki ya jinjina ma wannan kwamitin da ya gudanar da wannan aikin da cewa sun yi namijin ƙoƙari na ganin anyi nasarar kammala aikin da aka basu.

Ya yi kashedi akan yadda ake kiran hawan sallah da suna hawan bariki, inda wanda shi ne al’ada ta san shi da shi.

By ukarofi