APC a Katsina ta tabbatar wa Sirajo Kwaskwaro da takarar majalisar dokoki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jam’iyar APC ta tabbatar wa Sirajo Abdu Kwaskwaro da takarar kujerar majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Kaita a jihar Katsina.

Shugaban kwamitin fidda ‘yan takarar wanda harwala yau shine shugaban ƙaramar hukumar Kaita Injiniya Bello Lawal Yandaki ya sanar tare da ƙaddamar da ɗan takarar.

Ya ce samun nasarar kwaskwaro ya biyo bayan tsarin da uwar jam’iyar APC ta bi na gudanar da sasancin a tsakankanin ‘yan takarar da nufin fidda guda ɗaya.

Injiniya Bello Yandaki wanda ke riƙe da muƙamin shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙasa ya tabbatar wa alummar ƙaramar hukumar Kaita cewa da shi da sauran zaɓaɓɓun shugabanni da ‘yan takarar a matakai daban daban za su cigaba da kawo wa yankin ayyuka na cigaba a ƙaramar hukumar.

Shima a jawabin sa kwamishinan ƙasa da safayo Dr Faisal Umar Kaita ya jawo hankali waɗanda suka shiga takarar amma Allah bai ba su nasara ba da su sani neman hakki ba aibi bane amma su yi ƙoƙari su sanya buƙatar jam’iya a gaba.

A jawabin sa Kwaskwaro wanda zai tsaya zaɓen a karo na biyu ya yi kira da abokan takarar da ba su sami nasara ba da su zo a tafi tare domin cigaban ƙaramar hukumar da jihar baki ɗaya.

“Lokaci ne na mu yafe wa juna muzo mu tafi tare don cigaban yankin,”inji Sarajo Kwaskwaro.

Ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗ da irin abubbuwar raya ƙasa da gwamnatin sa ta kawo a ƙaramar hukumar ta Kaita.

By ukarofi