
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Kamfanin First HoldCo kuma hamshaƙin attajirin nan na kudancin Nijeriya, Femi Otedola, ya bayyana shirinsa na zuba jarin Dala miliyan 100, wato kwatankwacin Naira biliyan 137 a Matatar Ɗangote.
Otedola ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da ya jagoranci tawagar HoldCo zuwa wata ziyara a matatar.
Wannan ci-gaba na zuwa ne ƙasa da kwana bakwai da hamshaƙin ya musanta rahotannin da ke cewa shi ya ɗauki nauyin aikin gina matatar fetur ɗin Ɗangote.
A lokacin ne kuma ya warware batun ta kafar X, inda ya ce bai bada kuɗi don gina kowace matata ba, yana mai haƙiƙancewa akan “ko kwabo, dala ko naira” bai bayar ba don aikin.
Haka ma rukunin kamfanonin Ɗangote, wanda ya yi watsi da jita-jitar, inda ya ce an yi nasarar aikin gina matatar ne daga kuɗaɗen aro da aka samu daga fitattun ‘yan kasuwa a Nijeriya.
A lokacin ziyarar tasa ne, Otedola ya bayyana muradinsa na sayen hannun jari a matatar domin faɗaɗa harkokin kasuwancinsa.
