Daga MOH’D BELLO HABIB a Zariya
Akalla leburori uku ne suka jikkata sakamakon rushewar wani ɓangare na babban masallacin Juma’a da ake ginawa a Zariya da ke jihar Kaduna na Sarkin Zazzau.
Wasu shaidu da suka ga abin da ya faru sun ce an yi gaggawar kai waɗanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke Zariya domin samun kulawar likitoci.
Manhaja ba ta samu jin ta bakin injiniyan da ke kula da aikin ginin ba, domin wasu daga cikin mutanen da ke wurin sun bayyana cewa yana cikin waɗanda suka yi gaggawar kai waɗanda suka jikkata asibiti.
Kakakin Masarautar Zazzau, Abdullahi ƙwarbai, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.
ƙwarbai ya ce masarautar ta kafa kwamitin da ke kula da aikin ginin masallacin, wanda kuma ya bai wa wani kamfani kwangilar aikin.
“Masarautar ba za ta ce komai ba a halin yanzu dangane da abin da ya faru,” inji shi. Ya ƙara da cewa an gudanar da bikin ɗora tubalin ginin kafin a fara aikin.
Rushewar ginin ya haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna garin, inda da dama ke kira da a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin, tare da ɗaukar matakan da za su hana aukuwar makamancin haka a nan gaba.
“Wannan rushewar ta faru ne tun kafin a kammala ginin. Me zai faru idan ginin ya rushe yayin da mutane ke cikin masallaci suna sallah, kamar yadda ya taɓa faruwa a tsohon masallacin?” inji wani mazaunin garin, Murtala Baba.
Baba ya ce ya kamata a tabbatar da cewa ƙwararrun masu aikin gini ne kawai ake ɗora wa irin waɗannan manyan ayyuka.
Idan ba a manta ba, a watan Agustan 2023 ne Manhaja ta wallafa rahoton mutuwar mutane huɗu sakamakon rushewar wani sashe na masallacin da ke fadar Zazzau.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamali, ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin, sannan aka gudanar da jana’izar mamatan a fadar da misalin ƙarfe 8 na daren Juma’a.
Sarkin ya bayyana cewa ana shirin gyaran masallacin ne lokacin da lamarin ya faru, inda daga bisani ya umarci masu sallah su ci gaba da gudanar da sallah a harabar masallacin har sai an kammala gyaran.
Wasu mazauna yankin da suka zanta da Manhaja sun ce ginin ya rufta ne a lokacin sallar la’asar, yayin da masallata ke cikin masallacin.
Tarihi ya nuna cewa tsohon Masallacin Sarkin Zazzau Mallam Abdulkarim ne ya gina shi a shekarsr 1836 kimanin shekara 190 kenan.
