Kwankwaso na yi wa Tinubu aiki a ɓoye gabanin 2027 — Sanusi Bature

Spread the love

Daga RABIU MUHAMMAD a Kano

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aiki a ɓoye domin shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027.

Sanusi Bature ya kuma bayyana cewa haɗakar siyasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba za ta yi tasiri ba, musamman a jihar Kano.

Da yake magana a wata hira da ya yi a shirin Morning Show na tashar Arise Teleɓision ranar Laraba, Bature ya ce Jam’iyyar NNPP ba ta da ƙarfin da za ta iya tunkarar zaɓen 2027 ita kaɗai.

A cewarsa, an gudanar da tattaunawa tsakanin manyan jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya domin nemo mafita mai ɗorewa kafin zaɓen 2027, inda aka fara nazarin yiwuwar haɗaka da jam’iyyar APC mai mulki.

“NNPP ba ta da ƙarfin da za ta iya zama babbar jam’iyya a 2027. An cimma matsaya tsakanin manyan masu ruwa da tsaki ciki har da Rabiu Kwankwaso cewa dole ne a nemo wata mafita saboda NNPP ba za ta iya cin zaɓe ita kaɗai ba,” in ji shi.

Bature ya ƙara da cewa da amincewar Kwankwaso ne suka tuntuɓi Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC domin tattauna yiwuwar komawa jam’iyyar tare da shiga gwamnatin tarayya.

“Da yardar Kwankwaso muka tuntuɓi Tinubu da APC a matsayin zabinmu na farko domin duba yiwuwar shiga jam’iyyar da kuma samun damar shiga majalisar zartarwa ta tarayya,” ya bayyana.

Ya kuma yi zargin cewa Kwankwaso ya nemi ganawa kai tsaye da Shugaba Tinubu domin tattaunawar siyasa, amma daga bisani ya fasa bayan an tsara ranar ganawar.

“Kwankwaso ya dage cewa sai ya gana da Shugaba Tinubu kafin a yanke wata shawara kan sauya sheka. Amma bayan an sanya ranar ganawar, sai ya ce zai tafi China, daga nan kuma bai sake tsara wata ranar ba,” inji Bature.

Dangane da rade-radin haɗakar Peter Obi da Kwankwaso kuwa, Sanusi Bature ya ce irin wannan tikiti ba zai samu karɓuwa a Kano ba.

“Tikitin Peter Obi da Kwankwaso abin mamaki ne a Kano. Kwankwaso mai digirin PhD ya zama mataimakin Obi mai digiri na farko kawai, wannan ba irin Kwankwason da muka sani ba ne. Ban ga wannan haɗaka za ta yi nasara ba,” ya ce.

Bature ya kuma bayyana cewa sauye-sauyen siyasa za su ci gaba da faruwa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, yana mai cewa jam’iyyu da ’yan siyasa na sake tsara matsayinsu.

Ya yi zargin cewa mafi yawan magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya sun koma APC, lamarin da ya rage ƙarfin siyasar Kwankwaso.

“Yanzu Kwankwaso ya rage shi kaɗai. Wataƙila yana da kaso 30 zuwa 40 cikin ɗari na mabiyansa bayan sauya shekar da muka yi. Yanzu kusan kaso 70 cikin ɗari na magoya bayan Kwankwasiyya sun koma APC,” inji shi.

Ya ƙara da cewa tikitin Obi da Kwankwaso ba zai iya samun ƙuri’u miliyan ɗaya a jihar Kano kamar yadda NNPP ta samu a zaɓen 2023 ba.

“Kwankwaso shi kaɗai a ƙarƙashin NNPP ya samu sama da ƙuri’u miliyan ɗaya a Kano a 2023. Amma a 2027 idan Obi ne ɗan takarar shugaban ƙasa, Kwankwaso kuma mataimaki, wannan tikitin ba zai samu ƙuri’u miliyan ɗaya a Kano ba,” ya ƙara da cewa.

By ukarofi