Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani mutum mai suna Newton Isokpehi, wanda ya bayyana kansa a matsayin jami’in Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya mai shekara 26 yana aiki, ya yi barazanar kashe duk wanda ya ɗauke shi bidiyo yayin da yake bakin aiki.
Barazanar ta fito ne a cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda mutumin ya kuma yi kalamai masu zafi kan jama’a da kuma duk wani babban jami’i da yake zargin ya bayar da umarnin a riƙa ɗaukar jami’an ’yan sanda bidiyo yayin aiki.
Isokpehi ya yi kalaman nasa ne da Turancin Pidgin, kafin daga bisani aka fassara su zuwa Turanci.
Rahotanni sun nuna cewa yana amfani da wani asusun TikTok mai suna “Newton isokpehi for life” tare da sunan mai amfani #actor459, inda yake wallafa bidiyoyi sanye da kayan aikin ’yan sanda tare da wasu abubuwan rayuwarsa.
Ko da yake an goge bidiyon daga shafin nasa, har yanzu asusun yana nan a buɗe yayin haɗa wannan rahoto, tare da wasu tsoffin bidiyoyinsa cikin kayan ’yan sanda.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ko Isokpehi har yanzu jami’in Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ne ba.
A cikin bidiyon, mutumin ya ce: “dak ranar da nake bakin aiki a matsayin ɗan sanda, ina ɗauke da bindiga ina aikin gwamnati, wani ya kuskura ya zo yana ɗaukar bidiyo. Wannan ogan da ya ba ku umarnin ku riƙa ɗaukar mu bidiyo shi ne zai je jana’izarku. Shi ne zai binne ku. Duk adadin mutanen da zan kashe, shi ne zai binne su.”
Ya ci gaba da ƙalubalantar duk wanda ya isa ya nufo shi da kyamara yayin da yake aiki.
“Na yi shekara 26 ina aikin ɗan sanda a wannan wajen da muke shan wahala. Muna wahala kullum.
“Duk wanda yake ganin ya isa, ya kawo kyamararsa. Ya zo duk inda nake ya ɗauke ni bidiyo. Idan bai yi hankali ba, zan halaka kowa, har mutanen cikin mota da duk wanda yake kusa. Na rantse da Allah idan ban yi ba, Allah ya ɗauki raina,” inji shi.
Isokpehi ya kuma yi barazana ga duk wani babban jami’in ɗan sanda da ya bayar da umarnin a riƙa ɗaukar jami’an ’yan sanda bidiyo yayin aiki.
“Wannan ogan ɗan sandan da ya bayar da umarnin a riƙa ɗaukar jami’an ’yan sanda bidiyo, zan gallaza muku sosai. Za ku ga wahala. Matsala za ta lalata zuriyarku,” ya faɗa.
A cikin bidiyon mutumin ya nuna wani rauni a hannunsa wanda ya ce harbin bindiga ne ya jawo, yana mai cewa hakan shaida ce ta irin wahalar da jami’an tsaro ke sha ba tare da samun isasshen kulawa ba.
“Kun ga kamar haka aka haife ni? Wannan raunin harbin bindiga ne,” ya faɗa yana nuna hannunsa.
“Muna aikin gwamnati ne kawai. Biri na aiki, gwaggon biri na cin moriya. Jikina cike yake da raunukan harsashi da harbin bindiga, amma har yanzu muna cikin wahala,” inji shi.
Duk da kalaman nasa masu tsauri, Isokpehi ya yaba wa Sufeto Janar na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya na yanzu bisa fara biyan wasu haƙƙoƙin inshora da alawus-alawus na jami’an da suka mutu da iyalansu.
“Ku dubi iyalan wasu jami’an da suka mutu shekaru da suka wuce. Tun lokacin da wannan Sufeto Janar ya hau mulki yake fara sakin kuɗaɗen inshora da haƙƙoƙinsu,” ya ce.
Bidiyon, wanda aka ɗauka yana magana kai tsaye da kyamara tare da rubutun “God bless police” a sama, ya bazu sosai a kafafen sada zumunta.
Tun bayan bazuwar bidiyon, ’yan Nijeriya da dama sun yi tir da kalaman barazanar da mutumin ya yi, tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa tare da ɗaukar matakin da ya dace.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
