Sama da fatake 1,100 sun yi tattaki zuwa Kano daga Nijar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimamin fatake ‘yan Nijeriya sama da 1,100 ne suka isa Kano daga Agadez a Jamhuriyar Nijar ta hanyar tattaki, kamar yadda Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ta bayyana.

Hukumar ta ce, an zuba jami’an hukumomin tsaro a matakin ƙasa da jiha domin kula da su da sadar da su ga iyalansu.

Kwamandan na Makarantar Horar da Jami’an Shige da Fice, Anthony Akuneme, ya bayyana cewa tuni aka ɗauki dukkan bayanan da suak dace akansu domin tabbatar bin dukkan ƙa’idojin da ake buƙata gabanin damƙa su ga makusantansu.

Cibiyar tantance ƙasashen ɗaiɗaikun mutane ta Kano MAKIA da ITSK su ne a yanzu ke aiki a matsayin wajen karɓar fatake da harkokinsu.

A cewar rahoton, za a yi aikin miƙa su ga iyalan nasu ne a tsakanin NIS, NAPTIP, hukumar kula da fatake ta ƙasa-da-ƙasa da sauran hukumomin gwamnati.

Agadez ta zama ɗaya daga cikin wuraren da fatake suka fi samun mafaka a duniya, inda dubunnan ire-iren mutanen ke bi a kowace shekara da sunan zuwa Turai daga Afirka musamman a tsakanin shekarar 2015 da 2018.

By Babaji