Ɗan kasuwa ya rasu yayin rikici da ɗansa a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan Sanda a Abuja ta fara bincike akan mutuwar wani ɗan kasuwa mazaunin Abuja mai suna Mista Adimike Godwin, wanda aka yi zargin an halaka shi ne a yayin wani rikici a gidansa da ke yankin Guzape a babban birnin tarayyar.

Wasu rahotanni da ake yaɗawa ta kafafen sada zumunta sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan sa’insa da ɗansa mai shekaru 19 da aka ce mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) ne ya soka masa wuƙa.

Saidai, jami’an hukumar ‘yan sandan ba su tabbatar da asalin sunan makashin ba ko ainihin abin da ya sabbaba faruwar al’amarin.

A cewar rahotanni, jami’an tsaro sun samu marigayin ne a halin munanan raunuka kwance cikin jini, inda daga nan suka gaggauta garzayawa da shi asibiti.

Daga bisani an tabbatar da rasuwarsa a Babban Asibitin Karu.

A yanzu rundunar ta ce ta kama makusantan mamacin kuka tana gudanar da bincike akansu.

Wannan al’amari ya janyo jimami da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane ke kira da a ƙara kula da lafiyar kwakwalwa, tarbiyya da kuma magance shaye-shaye acikin matasa.

By Babaji