Duk da tuhumar EFCC, Yahaya Bello ya samu takarar sanata a APC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC domin takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya, duk kuwa da yana da fayil a hukumar EFCC.

Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Dr. Sadiƙ Mohammed, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, inda ya ce tsohon gwamnan ya samu ƙuri’u 72,349, lamarin da ya ba shi nasara a kan abokan hamayyarsa mafi kusa, Ibrahim Yakubu Adoke wanda ya samu ƙuri’u 315 da kuma Momoh Yusuf Obaro da ya samu ƙuri’u 188.

A yankin Sanatan Kogi ta Yamma kuwa, rahotanni sun nuna cewa Sanata mai ci, Sunday Karimi, na kan gaba yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.

Hakan ya biyo bayan janyewar wasu manyan masu neman tikitin takarar, ciki har da Sanata Smart Adeyemi da Samuel Bamidele Aro, gabanin kammala zaben, lamarin da ya ƙara bai wa Sunday Karimi damar samun nasara.

A Kogi ta Gabas kuma, rahotanni sun nuna cewa Sanata mai ci, Jibrin Isah Echocho, na baya a sakamakon da aka fitar kawo yanzu.

An ce ya sha kaye a ƙaramar hukumarsa ta Dekina inda ya samu ƙuri’u biyu kacal, yayin da babban abokin hamayyarsa, Dr. Joe Erico Ameh, ya samu ƙuri’u 19,805.

Majiyoyin jam’iyyar sun bayyana Dr. Joe Erico a matsayin dan takarar da manyan masu ruwa da tsaki a jihar ke goyon baya.

A halin da ake ciki, wasu daga cikin manyan ‘yan takarar da suka haɗa da Muritala Ajaka da Jibrin Echocho sun soki yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin, suna masu cewa bai bi ƙa’idoji da tsarin jam’iyyar yadda ya kamata ba.

By ukarofi