Tsare El-Rufai salo ne na garkuwa da shi da tsangwamar siyasa – Iyalansa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Asiya El-Rufai, ta zargi jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da tsare mijinta ba bisa ka’ida ba bayan zaman kotu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.

Asiya ta ce matakin ya saba wa umarnin kotu da ke cewa tsohon gwamnan ya ci gaba da kasancewa a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC.

Da take magana da manema labarai a wajen ofishin DSS da ke Abuja, Asiya El-Rufai, wadda ta bayyana kanta a matsayin mata ta biyu ga tsohon gwamnan, ta ce lamarin ya jefa iyalinsu cikin firgici tare da zargin hukumomin tsaro da bibiyar su da kuma tsoratar da su.

“Yanzu muna rayuwa cikin tsoro kullum. Kowace rana ana mana barazanar cewa DSS za ta kai farmaki gidanku, ICPC za ta kai farmaki gidanku, ko ‘yan sanda za su zo. Ana bibiyar mu. Ana sauraron wayoyinmu,” inji ta.

A cewarta, tun da farko El-Rufai ya gurfana a gaban Mai Shari’a Joyce AbdulMalik ta Babbar Kotun Tarayya, inda kotun ta ba shi beli tare da dage sauraron karar zuwa ƙarfe 1 na rana.

Ta ce yayin hutun zaman kotun ne jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin kai shi ofishin DSS duk da cewa akwai umarnin kotu guda biyu daga Kaduna da suka ce ya kasance a hannun ICPC.

“Ya ce musu, ‘Ba zan sauka ba saboda akwai umarnin kotu guda biyu daga Kaduna da suka ce a tsare ni a ICPC. Me ya sa kuke kawo ni nan?’ Ya ce, ‘Ni ba kayan daki ba ne da za a riƙa motsawa,” inji ta.

Ta ƙara da cewa har zuwa lokacin da take magana da manema labarai, tsohon gwamnan ya ƙi fitowa daga motar da aka kai shi da ita harabar DSS.

Wannan sabon rikici ya biyo bayan martanin da ICPC ta yi a ranar Litinin kan zargin cewa ana hana Mr El-Rufai abinci, kulawar lafiya da kuma ziyartar iyalansa.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, ICPC ta bayyana zarge-zargen a matsayin “marasa tushe,” tana mai cewa tsohon gwamnan na samun kulawar lafiya da kuma damar ganin iyalansa bisa umarnin kotu.

Mai magana da yawun hukumar, John Odey, ya ce an bai wa Mr El-Rufai damar ganin likitocinsa na kansa ciki har da likitan hakora da kuma likitan ido karkashin kulawar jami’an tsaro.

Ya kuma ce cibiyar tsare mutanen da ICPC ke da ita na samar da ma’aikatan lafiya ga waɗanda ake tsare da su idan buƙatar hakan ta taso.

Shi ma ɗan tsohon gwamnan kuma dan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, ya ce gaba daya shari’ar tana da alaka da siyasa.

Ya soki sharuddan belin da aka gindaya wa mahaifinsa, yana mai cewa an tsara su ne domin su zama masu wahalar cikawa.

“Wa yake tsare mutum na tsawon kwanaki 91? Me ya sa sharudan belin suka kasance masu tsauri har babu wanda zai iya cikawa?” inji shi.

Ya kuma soki sharaɗin da ake zargin an saka na cewa sai wanda yake matakin Leɓel 17 a aikin gwamnati tare da gida a Asokoro ko Maitama ne zai tsaya masa.

“Wane ma’aikacin gwamnati ne yake da Naira miliyan 100?” ya tambaya.

Sanata Lawal Adamu wanda shi ma ya yi magana a wajen zantawa da ‘yan jaridan, ya buƙaci a saki tsohon gwamnan nan take, yana mai cewa El-Rufai ya dawo Nijeriya daga Alkahira da kansa bayan gayyatar ICPC.

“Yana wajen Nijeriya. An gayyace shi ta ICPC, kuma ya dawo daga Alkahira domin ya miƙa kansa. Muna kira da a sake shi nan take.

By ukarofi