Gwamnati ta horar da mutum 4,000 sana’o’in hannu a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ma’aikatar harkokin kasuwanci, tsare-tsare da fasaha MBIT dake jihar Kaduna ta bayyana cewa ɗalibai 4,000 na samun horo kan sana’o’in hannu a cibiyoyin ta da ta buɗe a jihar.

Shugabban inganta tsare-tsare da horo na ma’aikatar Noel Bali ya sanar sa haka wa manema labarai ranar Litini a garin Kaduna.

Bali ya shaida cewa Cibiyar ta fara aiki tun bayan da shugaban Kasa Bola Tinubu ya kadamar da wurin a shekara 2025.

Ya ce aiyukan cibiyar ya ingantu saboda goyan bayan da ta rika samu daga gwamnan jihar Uba Sani wanda hakan ya sa mutane a ciki da kewayen jihar sanin aiyukkan da cibiyar ke yi.

”Gwamnati ta bude cibiyoyin horas da mutane sana’o’in hannu a Rigachikun, Soba da Samaru Kataf a tsakanin watanni Yuni da Yuli 2025.

”A dalilin wannan mataki da gwamnati ta dauka ya sa aka shigar da sana’o’in hannu da dama cikin tsarin kwasa-kwasan da horar da ɗaliban NSƙF da za a yi amfani da su a cibiyoyin.

Bali ya kuma ce shirin horar da mutane sana’o’in hannu da ma’aikatar Ilimi na Gwamnatin Tarayya TɓET da gwamnati ta shigo da shi ya saka ɗalibai 220 da wasu 210 cikin shirin kuma suna samun horo a cibiyoyin dake Rigachikun da Soba.

Ya ce cibiyar ta kammala horas da rukunin daliban farko sannan tana jiran a aiko da rukunin na biyu na daliban.

Bali ya ce gwamnati ta kara daukan wasu sabbin malamai 60 domin inganta aiyukkan da ake yi a cibiyar.

Ya ce aikin kafinta, fulomba, filasta, fenti, welda, saka tiles na daga cikin sana’o’in hannun da ake koyarwa a cibiyoyin.

By ukarofi