Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Iyayen ƙananan yara 42 ’yan ajin raino da ’yan ta’adda suka sace daga makaranta a yankin Mussa da ke ƙaramar Hukumar Askira-Uab a Jihar Borno, sun koma ga yin addu’o’i domin neman kuɓutar ’ya’yansu.
A ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe ne mayaƙan Boko Haram suka kutsa a wata Makarantar Firamare da ƙaramar Sakandaren Gwamnati da ke ya koma Mussa, suka yi abin gaba da ƙananan yara 42, yawancinsu ’yan shekara 2 zuwa 5.
Bayan kimanin kwana biyar da sace yaran ba tare da jin ɗuriyarsu ba, iyayensu da malamai sun duƙufa roƙon Allah Ya kuɓutar da su.
A yayin taron addu’o’in da suka gudanar a harabar makaranar a ranar Litinin, iyayen yaran sun bayyana takaicin rashin samun wani bayani game da halin da yaran suke ciki.
ɗaya daga cikin iyayen yaran ya bayyana cewa, “Mai aukuwa ta riga ta auku kuma ba mu da ƙarfi ko dabara sai ga Allah, domin Shi kaɗai Zai iya ceto mana ’ya’yanmu.
“A wannan taro, mu bar batun zargi ko ɗora wa wani laifi, mu miƙa komai ga Allah, tabbas Zai amsa roƙonmu Ya dawo mana da su lafiya.”
ɗaya daga cikin uwayen yaran cikin hawaye, ta bayyana yadda lamarin ya girgiza ta. Ta ce, “Ina cikin tsananin tashin hankali saboda har yanzu yaran nan ba a dawo da su ba, kuma babu wani bayani.”
Wani malamin makarantar da bai so a ambaci sunansa ba, ya bayyana cewa ƙananan yaran da aka sace ba ainihin ɗaliban makarantar ba ne.
“Yayyensu mata ne kan zo da su makaranta, mu kuma, saboda mu ƙarfafa zuwan yara makaranta sai muka buɗe musu ajin ’yan raino.”
ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin cewa an abokiyar hamayyarta, wato ƙungiyar ISWAP ce ta yi garkuwa da ƙananan yaran ne a matsayin ganimar yaƙi.
Boko Haram ta ce mayaƙan ISWAP da suka ɓalle daga Boko Haram sun yi haka ne a matsayin harin ɗaukar fansa, bayan sun Boko Haram ta kai hari a yankin da suke.
Wata babbar majiyar tsaro ta ce, “ɓangaren Boko Haram sun kai wa ’yan ISWAP hari a yankin Tafkin Chadi, inda suka kashe mayaƙa da dama suka kira su daga mafakarsu, suka mamaye wurin na tsawon mako guda.
“Su kuma a matsayin ɗaukar fansa, sai suka kai hari a yankunan Boko Haram, kuma suka sace ƙananan yara ’yan raino a matsayin ganimar yaƙi daga ƙauyen Mussa da maƙwabtakansu da suke ƙarƙashin Boko Haram.”
Majiyar tsaron ta ce suna “ƙoƙarin tuntuɓar ISWAP, waɗanda ake kyautata zaton sun laɓe a Dajin Sambisa sakamakon tsananin luguden wuta da sojoji ke yi a yankin Tafkin Chadi, domin ceto ƙananan yaran.”
A cewar majiyar, mafarauta da ’yan banga da suk bi sawun ’yan ta’addan sun gano inda yake yada zango a ranar Lahadi da misalin ƙarfe ɗaya na rana, amma ba su samu ƙarin jami’ai da za su taimaka musu domin fuskantar ’yan ta’addan kai-tsaye.
Ta ƙara da cewa, mafarauta da ’yan banga “Sun kira suna neman taimakon ƙarin jami’ai da misalin ƙarfe 1 na dare, amma dakarun ba su samu isa wurin ba sai bayan awa biyar. A lokacin kuma ’yan ta’ddan sun riga sun wuce.”
Shugaban ƙungiyar Haɗin Kan Matasan Borno ta Kudu, Samaila Ibrahim Kaigama, ya bayyana abin da ya kira rashin kulawar gwamnati a matsayin babban abin da ke damun al’ummar yanki.
Ya soki gazawar gwamnati wajen mayar da martani kan lamarin, yana mai cewa tun bayan sace yaran babu wani gagarumin mataki da gwamnatin jiha ko ta tarayya ta ɗauka.
“Da a ce ni ne ke rike da wani mukamin gwamnati, da zan yi aiki tare da mutanen karkara domin tuntuɓa da fahimtar waɗannan mutane domin ceto rayukan waɗanda ƙananan yaran.
“Wasu na cewa muna goyon bayan biyan kuɗin fansa ga ’yan ta’adda. Ba haka ba ne. Amma idan sojoji ba za su iya ceto su ba, me zai hana a gwada wata hanya daban?” in ji shi.
Ya nuna takaicinsa cewa sama da mutum 400 da aka sace a Ngoshe har yanzu suna hannun waɗanda suka sace su, kuma gwamnati ba ta yi wani abu ƙwaƙƙwars ba domin kuɓutar da su.
Sai dai a ranar Lahadi Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin tabbatar da sakin yara 42 da aka sace.
Yayin ganawarsa da manema labarai a Maiduguri, kakakin Gwamna Babagana Umara Zulum Malam Dauda Iliya, ne ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin, Gwamna Zulum ke ci gaba da tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro, ciki har da jami’an soja da ’yan sanda, a matsayin wani ɓangare na kokarin haɗin gwiwa domin kubutar da wadanda aka sace tare da dawo da su cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce, “Tun bayan aukuwar lamarin, Gwamna Zulum ya gudanar da jerin taruka da hukumomin tsaro domin tabbatar da ceto yaran makaranta da sauran waɗanda aka sace tare da haɗa su da iyalansu.”
