Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da haƙƙoƙin kundin tsarin mulki da kuma ’yancin addini da haɗin gwiwar addini.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi baƙuncin Daɓid Smith MP, Manzon Musamman na ƙasar Birtaniya kan ’Yancin Addini ko Imani, tare da Babban Jami’in Diflomasiyyar Birtaniya a Nijeriya, Richard Montgomery, a ofishin sa da ke Abuja.
A yayin ganawar tasu, Ministan ya ce Nijeriya tana ci gaba da kasancewa ƙasa mai alfahari da ƙabilu da addinai mabambanta, yana mai jaddada cewa ƙasar za ta ci gaba da girmamawa da kula da wannan bambancin a matsayin tushen ƙarfin jama’ar ta.
Idris ya bayyana matuƙar godiyar Nijeriya bisa ɗorewar goyon baya da haɗin kai da Birtaniya take ba ta, ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da abokan hulɗar ta na cikin gida da na ƙasa da ƙasa, tare da masu ruwa da tsaki, wajen ci gaba da yaƙi da tsattsauran ra’ayin addini da tashin hankali.
