Dangote ya ƙara jarin takin zamani a Habasha zuwa Dala biliyan huɗu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Attajirin Afrika kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya samu gagarumar tarba a birnin Gode na ƙasar Habasha yayin wata ziyara da ta shafi aikin kamfanin takin zamani da kamfaninsa ke gudanarwa a ƙasar.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ne ya karɓi baƙuncin Dangote, inda suka kai ziyara tare domin duba aikin ginin masana’antar takin zamani da ake shirin kafawa a ƙasar a ranar Lahadi.

Aikin ya samo asali ne daga yarjejeniyar masu hannun jari da gwamnatin Habasha da rukunin kamfanonin Dangote suka sanya hannu a kanta a watan Agustan bara, domin kafa masana’antar urea mai ƙarfin samar da tan miliyan uku a duk shekara. An fara aikin ginin ne a hukumance a watan Oktoban shekarar 2025.

An tsara haɗin gwiwar ne ta yadda Dangote Group zai mallaki kaso 60 cikin 100, yayin da kamfanin Ethiopian Investment Holdings zai mallaki kaso 40 cikin 100.

A yayin ziyarar, Dangote ya sanar da ƙara yawan jarin aikin daga dala biliyan 2.5 zuwa sama da dala biliyan 4, yana mai cewa an faɗaɗa tsarin aikin fiye da yadda aka tsara tun farko.

Cikin wata sanarwa da Dangote ya fitar, an bayyana cewa sabon tsarin aikin ya haɗa da shimfiɗa bututun mai mai tsawon kilomita 110, gina tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 120, cibiyar shirya kayan marufi na polypropylene, da kuma masana’antar haɗa takin NPK mai ƙarfin tan miliyan biyu.

Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin ginshiƙi na dabarun ci gaban Habasha, yana mai jaddada muhimmancinsa ga noma, wadatar abinci da bunƙasa masana’antu.

Ya ce, idan aka kammala aikin, masana’antar za ta ƙarfafa samar da taki a cikin gida, rage dogaro da shigo da taki daga ƙasashen waje, samar da ayyukan yi tare da tallafa wa miliyoyin manoma.

Abiy ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda aikin ke tafiya bayan zagaya wurin tare da Dangote, yana mai cewa an samu ci gaba mai kyau a sassa daban-daban na aikin.

A cewarsa, haɗin gwiwar na nuna cikakken jajircewa da kyakkyawan tsari tsakanin ɓangarorin biyu wajen aiwatar da wani babban aikin masana’antu na ƙasa.

Rukunin kamfanonin Dangote ya sake jaddada cewa aikin na daga cikin manufofinsa na bunƙasa masana’antu da kawo sauyin tattalin arziki a nahiyar Afrika baki ɗaya.

By ukarofi