
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon. Yakubu Danladi Salihu ya lashe zaɓen fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Juma’a.
Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin gwamna na jihar a jam’iyyar, Sanata Musliu Obanikoro yayin sanar da sakamakon, ya ce Hon. Danladi-Salihu ya samu ƙuri’u 94,000, lamarin da ya ba shi damar doke ‘yan takara takwas a zaɓen.
Shugaban kwamitin zaɓen ya kuma yaba wa mambobin jam’iyyar bisa fitowa ƙwansu da ƙwarƙwata duk da cewa an ɗage zaɓen daga Alhamis zuwa Juma’a.
Ya ƙara da cewa, yin zaɓen cikin lumana ya nuna yadda jam’iyyar ta shirya wa babban zaɓen 2027 domin ganin ta cimma nasarori a matakai daban-daban.
Sakamakon da aka fitar ya nuna cewa Ambasada Yahaya Seriki, wanda shi ne na hannun daman gwamnan jihar, ya samu ƙuri’a 41,700 votes, yayin tsohon shugaban APC na jihar, Bashir Omolaja Bolarinwa ya samu 22,118.
Sauran ‘yan takarar sun haɗa da Olufemi Kolawole Sani da ya samu 5,919; Dakta Ibrahim Yahaya Oloriegbe, 3,910; Mohammed Dele Belgore (SAN), 3,411; Dakta Alabi Oluwatoyin, 1,999; Mohammed Omar Bio, 1,122; da kuma Tajudeen Audu Abdulkadir mai ƙuri’a 1,462.
Haka kuma, akwai Azeez Salako Muhideen mai guda 1,198; Farfesa Olawale Adeniyi Sulaiman, 2,434; Ahmad Ibrahim Mahmoud, 362; Yetunde Musliat Adebowale, 638; Ahishat Ahmad Pategi, 1,734; da kuma Farfesa Abubakar Olarewaju Sulaiman, 1,722.
