Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta kama mutane bakwai bisa zargin sace da garkuwa da yaro ɗan shekara takwas wanda ke kan hanyar sa na zuwa makarantar Islamiya a cikin garin Katsina.
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na hukumar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar,ya bayana sunan Nura Aliyu ɗan shekara 39 a matsayin shugaban mutanen da ake zargi wanda kuma maƙwabcin yaron da su kai garkuwa da shi.
Ya ce sauran mutane shida da aka kama akwai Abubakar Aminu ɗan shekara 37 da Ibrahim Muhammad mai shekara 27 da haihuwa da Abdullahi Isma’il ɗan shekara 30 da kuma Iliyasu Sanusi mai shekara 51 akwai Abdul wanda yayi ɓatan dabo.
DSP Abubakar Aliyu ya bayyana cewa wadanda ake zargi sun nemi iyayen yaron da su biya maira miliyan 50 kafin su sako yaron,sai da a cewar jami’in yaɗa labarai bayan ya ce iyayen yaron sun biya Naira miliyan 17 ga mutanen kafin a sako yaron.
DSP Aliyu ya ce bayan da kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar ya sami bayanan sirri game da lamarin nan take ya turo wata rundunar na musamman VCRU ta shiga farautar ɓarayin har sai da suka zo hannu.
Bayan bincike a kan waɗanda ake zargi,’yan sanda suka gano mota kirar Peugeot 307 da babur na hawa da kuma kuɗi Naira miliyan 7.5 da ake zargi cikin kudin da suka karba a matsayin kuɗin fansa.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar ya yabawa yan sanda bisa ƙoƙari da ƙwarewa da suka nuna wajen kama waɗannan miyagun mutane.
Ya sha alwashin ganin rundunar sa ta magance ayyukan ɓata gari a jihar tare da sanarwa cewa da zaran sun kammala bincike za su gabatar da waɗanda ake zargi za a gurfanar da su a gaban kotu.
