
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADC tsagin su Nafiu Bala Gombe, ya kammala tantance masu neman takara gabanin zaɓen fidda gwani da za ta gudanar a faɗin Nijeriya.
Jam’iyyar ta bayyana cewa, an amince da mutane 1,657 su shiga zaɓen fidda gwani, yayin da aka kori mutum 212 saboda rashin cika sharuddan da aka gindaya.
Ta ce, an gudanar da tantancewar ne cikin tsari da gaskiya a jihohi 36 da Abuja, inda aka kafa kwamitocin tantancewa bisa kundin tsarin jam’iyyar da dokokin zaɓe.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa, ‘yan takara 980 ne aka tantance a matakin majalisun dokokin jihohi, waɗanda daga ciki aka soke 155.
Jagororin jam’iyyar ya bayyana cewa aikin tantancewar ya nuna yadda take ƙoƙarin aiki tuƙuru wajen tabbatar tsarin dimokuraɗiyya a matakin cikin gida, horo da bin ƙa’idoji wajen zaɓar ɗan takara.
Duk da ƙalubalen gasar tsare-tsaren jagoranci da shari’o’i akan gudanar da jam’iyyar, masu sharhi siyasa na ganin hakan a matsayin abin da ya ɗaga ta a fagen siyasa.
