Sojoji sun halaka ‘yan ta’adda, sun kama masu taimaka musu a Borno da Yobe

Spread the love

Dakarun tsaro na atisayen HAƊIN KAI sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ‘yan ta’adda a jihohin Borno da Yobe, inda suka halaka wasu da dama tare da kama masu taimaka musu wajen kai kayan tallafi.

Rahoton rundunar ya bayyana cewa an gudanar da hare-haren ne tsakanin 15 zuwa 21 ga watan Mayu.

A wasu samame da aka kai a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, dakaru sun kashe ‘yan ta’adda biyu bayan musayar wuta.

Haka kuma jami’an tsaro tare da mafarauta sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da satar shanu da taimaka wa ‘yan ta’adda wajen sayar da shanu domin samar musu da kudade.

Rundunar ta kuma ce matsin lambar hare-haren da ake kai wa maboyar ‘yan ta’addan ya sa wasu daga cikinsu da iyalansu suka fara mika wuya.

Kazalika, an samu mata da yara da suka miƙa kansu a Dikwa, yayin da wani matashi mai suna Babakaka Bukar ya miƙa bindigar AK-47 da harsasai ga sojoji bayan ya tuba.

A jihar Yobe kuwa, sojoji sun ƙwato bindiga da harsasai da wasu ‘yan ta’adda suka jefar yayin tsere wa farmakin dakarun tsaro.

By Babaji