Gwamnatin Katsina za ta horar da ɗalibai 300 kan fasahohin Web3 da Bockchain

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta hannun ofishin mataimaki na musamman ga gwamna kan ƙirkire-ƙirkire da fasaha, ta ƙulla wata yarjejeniya haɗin gwiwa da kamfanin Dar Blockchain mai hedikwata a ƙasar Tunisia, domin horas da ɗaliban manyan makarantu kan fasahohin Web3 da blockchain a faɗin jihar.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da haka a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa matasa, sauya fasalin harkokin zamani ta hanyar fasaha, da bunƙasa ci gaba mai dogaro da ƙirƙire-ƙirƙire.

Shirin zai ba matasa ƙwarewar da za ta dace da buƙatun zamani, tare da mayar da Jihar Katsina cibiyar fasahohin zamani masu tasowa a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

A matakin farko na shirin, za a horas da ɗalibai 300 daga manyan makarantu daban-daban da ke faɗin jihar.

Za a zaɓi mahalarta daga fannoni kamar kimiyyar kwamfuta, fasahar sadarwa, Injiniya, gudanar da kasuwanci, tattalin arziki, lissafi da kudi, banki da harkokin kuɗi, da sauran fannoni masu alaƙa.

Haka kuma, ɗaliban da ba na fannin fasaha ba amma suke da ƙwarin sha’awar harkokin fasaha za a yi la’akari da su.

Horon zai ƙunshi muhimman fannoni kamar tushen ilimin blockchain, tsarin Web3, smart contracts, aikace-aikacen da pps masu zaman kansu, kadarorin dijital, DeFi, tokenization, da tsaron blockchain.

Za a gudanar da horon ta hanyar haɗa koyon darussa ta yanar gizo, tarukan horaswa, atisayen aikace-aikace, da kuma jagoranci daga ƙwararru da abokan hulɗa na Dar Blockchain.

Da yake jawabi kan wannan shiri, mataimaki na musamman ga gwamna kan ƙirkire ƙirkire da fasaha, Ibrahim Adamu, ya bayyana cewa haɗin gwiwar ya yi daidai da manufar Gwamna Raɗɗa ta “Building Your Future”.

Ya ce an tsara shirin ne domin gina ƙwarewar fasaha tare da haɗa ɗalibai da damar ƙirƙire-ƙirƙire na duniya.

Ɗaliban da suka kammala shirin cikin nasara za su samu takardun shaida, jagoranci, da damar shiga horon aiki, gasar ƙirƙire-ƙirƙire (hackathons), da kuma damar aiki a tsarin blockchain.

By ukarofi