Yanzu-yanzu: Shugaban ma’aikatan Shugaban APC na Ƙasa, Mustapha Dawaki ya koma NDC ta su Obi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban ma’aikatan Farfesa Nentawe Yilwatda, Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, wato Mustapha Bala Dawaki, ya koma jam’iyyar adawa ta NDC.

Rahotanni sun bayyana cewa, Dawaki, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa a Jihar Kano ne, ya koma jam’iyyar ne ana ƙasa da mako guda da ya rasa damar samun tikitin takara bayan sulhun da aka yi acikin APC.

Mai taimaka wa ɗaya daga cikin jagororin NDC kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso akan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ya tabbatar da hakan a yau Litinin a wan saƙo da ya wallafa a kafar sada zumunta.

A cewarsa, ɗan siyasar ya koma jam’iyyar ne a gidan Kwankwaso da ke Miller Rose a Kano.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da NDC ke gudanar da shirye-shiryen zaɓar ‘yan takarar da za su wakilce ta a matakai daban-daban a jihar ta hanyar yin sulhu.

Saidai, ba a san ko Dawaki zai samu tikitin kai-tsaye ba na tsaya wa takara a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

By Babaji