
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Dakarun Tsaro na haɗaka na Arewa ta Gabas sashen Atisayen HAƊIN KAI, ta koka game da yiwuwar aukuwar munanan hare-haren mayaƙan Boko Haram da ISWAP da ke harin musamman wajen dandazon jama’a a shiyyar yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah.
Wannan gargaɗi na ƙunshe ne acikin wata sanarwa da hedikwatar ta aike wa manema labarai daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, wadda ke ɗauke da sanya hannun Kakakinta, Laftanal Kanal Sani Uba.
A cewar sanarwar, bayanan sirri da rundunar ta tattara sun nuna cewa akwai yunƙuri daga wasu mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da na ISWAP na su yamutsa hazo akan fararen hula a yayin da ake tsaka da shagulan sallar.
Ta ce, akwai yiwuwar mayaƙan su tura ‘yan ƙunar baƙin-wake da kuma dasa boma-bomai a wuraren da ke da taron jama’a.
Akan haka ne sashen ya shawarci al’ummar shiyyar da su gudanar da sallar idi a kusa da gidajensu da wuraren da suka saba da su tare da ƙaurace wa dukkan wani taron al’umma da ke bainar jama’a.
Haka kuma, ta yi kira a gare su da su kasance masu lura da sanya ido akan wuraren dandazo kamar kasuwanni, tashoshin mota, cikin bankuna da wuraren ibada.
Kazalika, sashen ya buƙaci al’umma da su ruwaito dukkan wani abin zargi da suka gani a inda suke cikin hanzari ga shingen bincike mafi kusa ko ofishin ‘yan sanda ko sansanin sojoji, yana mai kira da a ba jami’an tsaro haɗin kai yayin da suke sintiri a yankunan sassan shiyyar.
Har ila yau, hedikwatar ta roƙi jama’a da su ƙaurace wa yaɗa labaran ƙarya ko jita-jita da ka iya haddasa firgici acikin al’umma, tana mai kira ga kowane ɓangaren jama’a da ya bayar da haɗin kai yayin hidimar sallar.
