Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya ta bada hutun Babbar Sallah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba da Alhamis, wato 27 da 28 ga watan Mayu, 2026 a matsayin lokacin hutun Babbar Sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da haka ta ofishin Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani a wata sanarwa.

A cewar sanarwar, gwamnatin ta yi haka don girmama addinai da abin da miliyoyin al’ummar Nijeriya suka gada wajen yin biki da kuma al’ummar Musulmi a sassan duniya.

Tunji-Ojo ya kuma yaba wa al’ummar musulmi a Nijeriya da ma sauran ƙasashen duniya bisa zagayowar lokacin yana mai bayyana Eid-el-Adha a matsayin biki mai muhimmanci da ake jaddada sadaukarwa da biyayya ga ubangiji da kuma mutunta juna tsakanin al’umma.

Ministan ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in nema wa ƙasa zaman lafiya, tsaro da ci-gaba mai ɗorewa.

Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su ƙarfafa ‘yan uwantakar da ke tsakaninsu, haɗin kai da zaman lafiya a yayin bikin sallar.

A ƙarshe, gwamnatin tarayyar ta ce tana taya al’ummar musulmi murnar lokacin da kuma fatan a yi hidima cikin ƙoshin lafiya.

By Babaji