Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mutane 12 suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Kano zuwa Katsina, a kwanar Gidan Mutum Ɗaya, bayan wata mota ta hukumar sufuri ta jihar Katsina(KSTA) ta yi karo da wata tirela.
Mutane shida ciki har da direba sun mutu nan take, yayin da wasu shida suka rasu a asibiti.
Yanzu haka mutum biyu na karɓar magani, yayin da aka sallami wasu biyar bayan jinya.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana alhininsa kan lamarin tare da jajanta wa iyalan mamatan, sannan ya buƙaci masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya domin kauce wa irin haka a gaba.
