Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutane huɗu bisa zargin damfarar kujerun aikin hajjin shekarar 2026 tare da ƙwato kayayyakin hajji na bogi.
Waɗanda a ke zargin sun hada da Aminu Hassan Zauro da Tabi’u Abubakar, Usman Attahiru da Mustapha Sani Zauro. An kama su ne bayan ƙorafin da hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kebbi ta gabatar na Waɗansu maniyyata da sunayensu ba sa cikin rajistar hukumar yayin shirye-shiryen aikin Hajji.
Bayan gudanar da binciken ƙwakwaf ne aka gano Aminu Hassan Zauro ya karɓi Naira miliyan 8.6 daga wani mutum da sunan samar masa kujeru biyu na Hajji, duk da cewa ba shi da wata alaƙa da hukumar da ke bayar da guraben hajji. Haka kuma ya karɓi Naira 690,000 daga wani mutum ta irin wannan hanyar.
‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya bai wa Waɗanda ya damfara kayayyakin hajji na bogi da suka haɗa da jakunkunan Hajji, hijabai, zanen kaya da katinan bayanan lafiya na jabu domin ɓoye laifinsa. An kuma kwato wayar salula kirar Techno Android daga hannunsa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Umar M. Hadejia, ya gargaɗi maniyyata da sauran al’umma da su riƙa hulɗa da hukumomin da ya dace a duk lokacin da wani lamari ya shafi wata hukuma maimakon neman wani mutum don shiga tsakani domin kaucewa faɗawa hannun ‘yan damfara.
Yanzu haka dai waɗannan mutanen suna hannu yan sanda kuma da zarar an kammala bincike za a tura su kotu.
