Mene ne mafitar ’ya’yanmu?

Spread the love

A yau al’umma na cikin wani hali na damuwa da tashin hankali dangane da tarbiyyar yara da rayuwar matasa. Duk wanda ya kwatanta yadda yaran da suka gabata suka taso da yadda yaran yau ke rayuwa, zai fahimci cewa akwai babban sauyi mai cike da haɗari da ya mamaye tarbiyyar zamani.

A da, iyaye su ne ginshiƙin tarbiyya. Uba da uwa suna saka ido sosai kan rayuwar ’ya’yansu, suna koya musu kunya, biyayya, ladabi, da tsoron Allah. Yaro kan tashi ya san girman na gaba da shi, ya san mutuncin addini, ya san abin da ya dace da wanda bai dace ba. Makaranta, gida, masallaci da al’umma duk suna taka rawa wajen gina tarbiyyar yaro.

Sai dai abin takaici, yau abubuwa sun sauya. Wasu yara sun zama ba su jin magana, ba sa girmama iyaye ko malamai, ba sa jin tsoron aikata abin da bai dace ba. Ana ganin yara ƙanana suna shiga harkokin da suka fi ƙarfinsu, suna kwaikwayon rayuwar banza daga kafafen sada zumunta, fina-finai da wasu shirye-shiryen da ba su dace da tarbiyyar Hausawa da Musulunci ba.

A yau ana ganin wasu matasa da yara suna aikata abubuwan da a da ko tunaninsu ba ya yiwuwa a cikin al’ummar Hausawa da Musulmi. Za ka ga yaro yana ɗaga murya yana musu da iyayensa kamar sa’anni, ko ya yi wa mahaifinsa gardama a bainar jama’a ba tare da jin kunya ba. Wasu matasan ba sa gaishe da manya, ba sa tashi idan dattijo ya zo, kuma suna kallon ladabi tamkar tsohon salo ne da bai dace da rayuwar zamani ba.

A makarantu ana samun ɗalibai suna cin mutuncin malamai, wasu ma har da yin faɗa da malamansu ko ɗaukar bidiyonsu domin raini a kafafen sada zumunta. Haka kuma akwai matasa maza da mata da ke sanya tufafin da suka saɓa wa tarbiyya da addini, suna alfahari da hakan a bainar jama’a.

Wasu kuma sun fi ɗaukar mashahuran mawaƙa da ’yan TikTok a matsayin abin koyi fiye da malamai da mutanen kirki. Abin takaici, idan aka yi ƙoƙarin gyara wasu daga cikinsu, sai iyaye su ce “yara ne na zamani” ko “haka rayuwa take yanzu.” Alhali irin wannan sakaci na iya rusa tarbiyyar al’umma baki ɗaya.

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wasu iyaye ke goyon bayan irin waɗannan halaye. Maimakon su gyara yaransu, sai su kare su ko da sun yi kuskure. Wasu iyaye suna ganin cewa barin yaro ya yi duk abin da yake so shi ne wayewa, alhali hakan na jefa shi cikin halaka. Wasu ma suna tsoron tsawatar wa yaransu saboda kada su yi fushi ko su daina jin daɗin gida.

A wasu lokutan za ka ga yaro ko yarinya na shiga shafukan sada zumunta suna wallafa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya, amma iyaye na gani ba tare da sun ɗauki mataki ba. Wasu yara sun fi kusa da wayar hannu fiye da Alƙur’ani, sun fi sanin mawaƙa da ’yan wasan kwaikwayo fiye da tarihin Annabawa da Sahabbai.

A addinin Musulunci, tarbiyyar yaro babban amanar Allah ce a hannun iyaye. Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa kowane makiyayi za a tambaye shi abin da aka ba shi kulawa a kai. Idan iyaye suka yi sakaci wajen tarbiyyar yaransu, ba wai duniya kaɗai za ta sha wahala ba, har ma za su fuskanci hisabi a gaban Allah.

Rashin tarbiyya na haifar da matsaloli masu yawa a cikin al’umma. Daga ciki akwai rashin kunya, sata, shaye-shaye, zina, rashin girmama manya, da kuma aikata laifuffuka iri-iri. Yaro da bai samu kyakkyawar tarbiyya ba yana iya zama barazana ga iyalinsa da ma al’umma baki ɗaya.

A yau wasu iyaye sun mayar da hankali wajen tara dukiya da neman kuɗi, amma sun manta da kula da tarbiyyar yaransu. Wasu ba su san irin abokan da yaransu ke hulɗa da su ba. Wasu ba sa sanin inda yaransu ke zuwa ko abin da suke kallo a waya. Wannan sakaci na daga cikin manyan dalilan lalacewar tarbiyyar zamani.

Mafita kuwa tana hannun iyaye da al’umma gaba ɗaya. Dole iyaye su dawo kan turbar tarbiyya irin ta addini da al’adun gari. Dole a koyar da yara tsoron Allah tun suna ƙanana. Dole iyaye su zama abin koyi ga yaransu ta fuskar ɗabi’a da mu’amala. Ba za ka hana yaro wani abu ba alhali kai kanka kana aikata shi.

Haka kuma, ya kamata a rage yawan barin yara da wayoyin hannu ba tare da kulawa ba. Yaro na buƙatar lokaci tare da iyayensa, nasiha, kulawa da kuma koyarwa. Idan aka bar kafafen sada zumunta su zama malamansa, to akwai babban haɗari.

Malamai ma suna da rawar takawa wajen wayar da kan iyaye da yara game da muhimmancin tarbiyya. Haka gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da addini su ma suna da alhakin samar da hanyoyin da za su taimaka wajen gyara tarbiyyar matasa.

Mafitar hakan ita ce iyaye su dawo da tsattsauran kulawa cikin hikima da soyayya, su sanya ido kan abokan hulɗar yaransu da abubuwan da suke kalla ko bi a kafafen sada zumunta. Haka kuma dole ne a koyar da yara muhimmancin girmama manya, kunya, da ladabi tun suna ƙanana, tare da hukunta duk wani hali na rashin ɗa’a cikin adalci. Idan gida, makaranta, malamai da al’umma suka haɗa kai wajen dawo da tarbiyya, za a iya rage wannan matsala kafin ta ƙara lalata rayuwar matasanmu da makomar al’umma baki ɗaya.

Mu tuna cewa tarbiyya ita ce tushen ci gaban al’umma. Duk al’ummar da tarbiyya ta lalace a cikinta, to komai yawan arzikinta ko iliminta ba za ta samu zaman lafiya da ci gaba na gaskiya ba.

Allah Ya shiryar da ’ya’yanmu, Ya ba iyaye ikon sauke amanar tarbiyya yadda ya dace. Amin.

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.

By ukarofi