
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu JAMB, ta ayyana ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2026 a matsayin lokacin gudanar da jarabawar UTME ga ɗaliban da ba su samu damar rubutawa ba duk da cewa an tantance su.
Kakakin JAMB, Fabian Benjamin ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Litinin.
A cewar hukumar, za a yi haka ne domin ba wa ɗaliban da suka fuskanci tsaikon sadarwa da wasu matsalolin yayin ainihin lokacin rubuta jarrabawar.
A tsakanin ranakun 23 ca 29 na watan Afrilu, 2026 ne aka gudanar da jarrabawar a cibiyoyin JAMB na faɗin Nijeriya, inda wasu suka fuskanci matsalolin sadarwa wajen rubuta jarrabawar.
Haka kuma, JAMB ta ce matakin nata zai shafi dukkan waɗanda ta gano sun samu tsaikon kuma ta zayyano sunayensu.
Ta ƙara da cewa, ɗaliban da suak je rubuta jarrabawar da na’ura ta gaza tantance su, su ma ta sanya su a jerin waɗanda za su rubuta jarrabawar.
